Yadda Zaki Gyara Girkin Ki

0 779

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

HANYOYIN KARE KAI A KICIN DINKI

Wannan hanyoyi da zan kawo su a kasa zasu baki damar gyara abincinki yayin da yasamu wata matsala.

Kada ki ajiye Albasa da Dankali a tare saboda duka biyu sun samar da iska wacce take haifar da ɗaya daga cikinsu lalacewa da sauri sauri.

Ki Sanya ganyen lemo biyu ko uku a cikin manki da zaki soya, kibari har sai ganyen yay baki sanan ki cire shi. Hakan kansa manki yazama kamar asalin na man da aka tace daga gyada, sanan manki zaiyi dadi yayin sawa a abinci.

Don nisantar da hanyenki daga zafin barkono ko attaruhu da kike yayanka, idan kinzo wanke hanun saiki sanya gishiri da manja saiki wanke sosai bazaki kara jin zafinba.

Idan tsautsayi yasa gishiri yayi yawa a miyarki saiki dan sanya dankalin turawa a ciki, wannan dankali zai janye wannan gishiri kuma miyarki zatayi daidai.

Idan miyarki ta kwana zaki kuma soyata saiki dan samu gawayi ki dan saka a ciki dandanon miyarki zai dawo kamar sabuwa, idan kin sauke miyar saiki cire gawayin.

Kada ki sanya yayan itace kamar su (Lemon Zaki, Lemon tsami ko tumatir) da dai sauransu a cikin firji, saboda wannan sanyin na ciki kan sanya su rage dandano mai dadi.

Idan kina son amfani da manki na girki batare da dandano ba a cikinsa, saiki samu citta kamar kwaya hudu (4) saiki soya man da ita , tozai cire duk wani kamshi dake cikin man.

Kiturawa yan uwa mata don su Amfana.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »