Yadda Zaki Hada Mayonnaise Da Kanki

0 5,275

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

MAYONNAISE

Yar Uwa memakon siyan Mayonnaise da kikeyi mai zai hana bazaki hada naki da kanki ba don kaucewa asarar kudi ga mai gidanki.

Abubuwa kadan zaki nema don yin hakan.

ABUBUWAN BUKATA:

  • Kwai Kamar Uku (3)
  • Lemon Tsami (1)
  • Sukari cokalin shayi rabi 1/2 (Optional)
  • Gishiri Kadan.
  • Farin Mai.

YADDA ZAKI HADA:

Kisamu Blender dinki mai kyau saiki kawo kwanki ki fasasu a ciki, sai lemon tsami dinki ki yanka shi saiki matse ruwan a cikin blender din wato inda kika fasa kwanki, saiki kawo manki mai kyau shima kizoba a ciki, saiki saka gishiri kadan a ciki.

Shi kuma sukari optional ne idan kinga dama basaikin saka ba idan kuma kinaso to dan kadan zakisaka a ciki, saikiyi ta markadashi a blender dinki har sai yayi kauri shikenan kawai sai ci da bread.

Bawani wahala aci dadi lafiya.

please ki turawa yan uwa don suma su amfana.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »