Wannan shine cigaban bikin takutaha a Kano na 3
RIJIYAR TAKU
Rijiyar Taku wata rijiya ce da take tsakiyar unguwar Madabo. Taku kuwa sunan wata mata ne da ta rayu a wannan unguwa. Mahaifinta shi ne Malam Usman Attuman, babban waliyyin nan da ya zauna a Unguwar Madabo. Ita Taku a lokacin da zo rasuwa ne, ganin ba ta da da ko daya, sai ta dauki kundin karatunta da wanda ta gada a wajen babanta, sai ta zuba a wannan rijiya.
Bayan rasuwar Taku, duk mutumin da ya sha ruwan wannan rijiya, sai Allah ya ba shi basira ta karatu cikin qanqanin lokaci. Haka kuma, duk mara lafiyar da ya sha ruwan rijiyar, sai Allah ya ba shi lafiya. Idan kuma ciwon a fili yake, idan aka shafa a wurin sai ya warke. Wannan al’amari ne ya sa, a duk lokacin bikin takutaha, mutane kan zo domin samun ruwan wannan rijiya ta Madabo. Hatta wadanda ba su sami damar zuwa ba, sukan aiko da mazubi a dibar musu ruwan (Hira da, M.B.R:22/12/08).
Wannan ne ya sa a ranar takutaha wasu samari kan debo ruwan wannan rijiya a bokitai suna yawo da shi suna cewa:
“A sha a shafa, sadaka sai an niyya”
Baya ga haka, bayan tafiya ta yi nisa, akan taru a dinga leqa wannan rijiya ana jefa kudi, ana cewa wata taguwa ce take leqowa a duk wannan rana,sannan da zarar an gama karatun Madabo rana ta daga, sai ta koma har sai kuma wata shekarar.
HAWA DUTSEN DALA
Haqiqa hawa dutsen Dala a ranar da ake gabatar da bikin takutaha yana nuna alamun bikin Maguzawa da suke yi a Kano duk shekara, wanda suke hawa dutsen Dala da Gwauron Dutse da Magwan da Fanisau suna gabatar da bukukuwan bauta. Ganin cewa shi kansa bikin takutaha, malaman Madabo sun qirqire shi ne domin kawar da hankalin matasa da mata daga wadannan bukukuwa na Maguzawa, to da alamun shi ya sa har yanzu a duk ranar bikin takutaha samari da mata da yara suke yin dandazo wajen hawa wannan dutse na Dala.
Duk da cewar su Maguzawa suna gabatar da bautarsu ne bisa jagorancin shugabansu, wato Barbushe wanda yake shiga dakin Tsumburbura ya jiyo musu abin da zai faru a wannan shekarar, kuma ya fito ya sanar da su. A yanzu ba haka ba ne, domin kuwa sai bayan an gama karatun Madabo kuma babban malami ya yi addu’a an watse. A sannan ne yara da samari suke tafiya domin hawa dutsen Dala. Don haka, ba sharadin bikin ba ne sai an hau wannan dutsen.
A kan Dala, ana gabatar da abubuwa ne da suka shafi nishadantarwa da kuma kallon qwaryar birnin Kano. Wasu har hotuna suke dauka. Daga baya, an samu cewar wasu ma suna hawa ne domin su yi shaye-shayen kayan maye da yin caca da kuma fadace-fadacen ‘yan daba wanda har ta kan kai da ji wa kai rauni. Wannan ba ya rasa nasaba da nason irin yadda maguzawan da suke yin bikinsu a kan dutsen Dalan suke yin shaye-shayen giya da sauransu. Don haka, ana iya kallon wannan gurbacewa a matsayin yadda bikin maguzawan na asali yake a gurbace.
MATSAYIN BIKIN TAKUTAHA
Bikin takutaha muhimmiyar rana ce a cikin garin Kano, domin a wannan rana akan yanke duk wasu huldodi a mayar da hankali wajen gudanar da wannan biki, musamman a wajen qananan yara. Dangane da wannan biki kuwa, wadansu suna ganin ba zai rasa alaqa da bautar gunkin Tsumburbura ba, wanda jama’ar Kano suke yi tun kafin zuwan addinin Musulunci (Ibrahim,1982:290).
Bukukuwan da Maguzawa suke yi a kan dutsen Dala yana matuqar jan hankalin mata da yara da baqi, don haka sai malaman Madabo suka hadu a masallacin Madabo suka shawarta kan yadda za su dauke hankalin masu zuwa kallon wadannan bukukuwa na Maguzawa.
Manya-manyan malaman wannan zamani da suka zartar da wannan shawara, sun hada da: Shehu Isa Mai Lawali da Shehu Mamuda mai Mudawwana da Shehu Ibrahim Liman Mai batta da Shehu Sulaiman mai rubutu da sauransu. Haka kuma, an sami wakilcin malamai daga unguwannin Dukurawa da Sheshe da Mandawari da Jujin-‘yanlabu da Madatai da sauransu (Hassan,1998:97).
Matsayin bikin Takutaha bai wuce ganin an kawar da hankalin yara da mata daga aqidar Maguzanci zuwa tarbiyyar musulunci ba. Wannan shi ne dalilin da ya sa Madabo suka kafa yin Mauludi a wannan unguwa, wanda daga baya ne mutane suka sauya masa suna zuwa Takutaha.
Dangane da sauran al’umma kuwa, wannan rana tana da matsayi sosai a wajensu. A wannan rana sukan sami damar ziyartar dangi wadanda aka dade ba a hadu ba. Baya ga haka, qananan yara sukan sami walwala da nishadi a wannan rana, musamman a kan Dala, inda ake kade-kade da raye-raye. Har wa yau, masu kayan sayarwa suna samun ciniki sosai, kasancewar jama’a suna zuwa daga bangarori daban-daban. Bugu da qari, al’umma suna haduwa don yi wa kawunansu da garinsu addu’o’i baki daya.
TASIRIN ZAMANI KAN BIKIN TAKUTAHA
Hausawa na cewa, “zamani riga, in ka gani sai ka saka”. Haqiqa bikin takutaha ya samu sauye-sauye da dama, sakamakon juyin rayuwa da kuma samuwar aloli sababbi na zamani.
Dangane da karatun Ishiriniya da akan gabatar a zamanin farko, karin Ishirin.iya ‘yar Madabo ake yi kawai, amma a yanzu, kowanne ma ana yi. Baya ga haka, a zamanin farko ba a yin karatun da amsa kuwwa, sannan babu wakilan kafofin watsa labarai, amma yanzu, bayan abubuwan da sukan dauka da kyamarorinsu, har sai sun nemi jawabai daga jami’an gudanar da taron, kwatankwacin yadda ake gudanar da taron zamani.
Baya ga haka, hawa dutsen Dala da yara suke yi, har suna leqa kogo da sauransu. A sakamakon tasirin da zamani ya yi a yau, yawanci a kan Dala babu abin da ake yi banda caca da shaye-shayen kayan maye da qwace ga qananan yara da kuma fadace-fadace tsakanin ‘yan daba.
Bugu da qari, kasancewar an samu bunqasar makarantun Islamiyya da yawaitar dalibai, a yau duk ranar takutaha daliban Islamiyyoyi da malamansu da mawaqa masu yabon Annabi Salallahu Alaihi wasallam sukan yi kewaye tun daga unguwar Madabo zuwa Gadar Salga zuwa Unguwar Qoqi, su kewayo Qofar Mazugal, su wuce Gwammaja, su dawo Unguwar Madabo. A cikin wannan kewaye da suke yi, suna gabatar da karatuttuka da waqe-waqe ne har su dawo.
KAMMALAWA
Bikin Takutaha, biki ne wanda ake gabatar da shi a garin Kano. Wannan takarda ta fito da yanayin wannan biki da matsayinsa da kuma canje-canje da suka shafe shi sakamakon ci gaban zamani. Daga nan, takardar ta fitar da yadda ake gabatar da bikin Takutaha da kuma irin matakan da ake bi wajen gudanar da shi. Misali, waqe-waqe na begen Annabi Salallahu alaihi wasallam, da barar takutaha da leqa rijiyar Taku da kuma hawa dutsen Dala.
MANAZARTA
Awai, K.S (1995) “Nazari a Kan Yadda ake Gudanar da Bikin Kalankuwa a Garin
Bomo ta Qasar Zaria” B.A. Dissertation, B.U.K.
Tsanyawa, S.A (1983) “Girman Asali Riqe Al’ada: Nazarin Wasu Bukukuwan
Hausawa Uku (Bikin Sallar Cika-ciki da Kalankuwa da Nadin Sarauta”. B.A Dissertation, B.U.K.
Yahaya, I.Y (1979) Oral Arts and the Socialization Process: A Socio-Folklore
Perspectibe of Initiation from Childhood to Adult Hausa Community Life, bol. 1, Kundin Digiri Na Uku.
CSNL (2006) Qamusun Hausa Na Jami’ar Bayero, Zaria: ABU Press.
Hassan, S.Y (1998) Madabo Jami’ar Musulunci, Kano Nigeria, Kano: Triumph
Publishing Company.
Ibrahim, M.S (1982) Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin Musulunci Kan
Rayuwar Hausawa ta Gargajiya, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.
Yahaya, I.Y. da Sani, MAZ da Gusau, S.M. da ‘Yar’adua, T.M (1992) Darussan
Hausa Don Manyan Makarantun Sakandare, Ibadan: Unibersity Press.
Bargery, G.P. (1934) Hausa-English and English-Hausa Dictionary, London:
Odford Unibersity Press.
WADANDA AKA YI HIRA DA SU
- Malam Adam Muhammad, ranar 11-12-08 a zaurensa na Unguwar Madabo.
- Malam Baba Rabi’u 22-12-08 a gidansa na Madabo.
Tijjani Shehu Almajir
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,
Jami’ar Bayero, Kano.