NAU’O’IN JIGO A WAKOKIN TASHE
Akwai abubuwa da yawa wadanda ake gina jigon wakokin tashe a kansu wadanda suka shafi rayuwar al’umma daban-daban, tun daga zamantakewarsu da mu’amalolinsu da sauran huldodin rayuwa. Dangane da wannan nazari, an gano nau’o’in jigo a cikin wakokin tashe kamar haka:
- Jigon Ban-dariya;
- Jigon Fadakarwa;
- Jigon Tarbiyya;
- Jigon Addini.
Da sauransu.
JIGON FADAKARWA A WAKOKIN TASHE
Fadakarwa na nufin fadakar da mutane kan wani abu marar kyau da suke aikatawa da su daina ko su gyara, ko su karfafa riko da wani aiki mai kyau.
Wakokin tashe masu dauke da jigon fadakarwa suna taimakawa wajen canza halayen mutanen da suke aikata ba daidai ba, walau bisa jahilci ko rashin mafadi.
Bargery (1934:288) ya bayyana ma’anar fadakarwa da “zaburar da fadakar da a sa mutum ya fahimta, a sanya mutum ya gano wani abu na hakika wanda aka rigaya aka mance”.
Ya ci gaba da cewa, fadakarwa takan ta da tsimin mutum”. ‘Yar’aduwa (2001:126) cewa ya yi, fadakarwa na nufin nusar da mutum a kan abubuwan da ya sani tun tuni da yi masa hannunka-mai-sanda, don ya dawo ya yi la’akari da su”.
Jigon fadakarwa abu ne da zai iya shafar rayuwa baki dayanta, sannan yana magana ne dangane da hani ko horo a kan wasu al’amura da al’umma suke gudanarwa a rayuwarsu ta yau da kullum (Chamo,2006:82).
A kan fadakar da al’umma a kan su rungumi kyawawan ayyuka masu ingantawa ko kuma su guji halaye marasa kyau kamar gulma da yaudara da lalaci da sauransu.
Akan fadakar da al’umma su nemi na kansu, ko dagewa a kan neman wani abu mai amfani a gare su da sauransu.
A dunkule, jigon fadakarwa ya kunshi abubuwa masu yawa a karkashinsa wadanda suka hada da gargadi da tarbiyya da nasiha da gyaran hali da hakuri da rikon amana da wayar da kai da kira ga a bar abubuwa munana da sauransu. Daga ciki akwai:
a.
Tsoho da gemu,
Amshi: Ya tsufa.
A tallabe shi,
Amshi: Ya tsufa.
A ba shi na Allah,
Amshi: Ya tsufa.
A taimake shi da dawa,
Amshi: Ya tsufa.
A agaza masa,
Amshi: Ya tsufa.
Wannan waka ta kunshi fadakarwa a kan sanya tausayi a zukatan yara da kuma tallafar mutumin da ya tsufa ko karfinsa ya kare.
A wajen aiwatar da wannan wasa na tashe, yara suna kwaikwayar shigar tsofaffi ta hanyar sanya farin gemu da saje ta yin amfani da auduga, sannan wanda ya yi wannan shiga zai dinga nuna gajiyawa irin ta tsofaffi ta hanyar takwarkwashewa da nuna rashin kwari, su kuma ragowar yara suna tallafar sa.
b.
Na ci na kasa tashi,
Amshi: Baba zari gareka.
Ai tuwon ne da dadi,
Amshi: Baba da sai ka daure.
In bar miyar har da nama?
Amshi: Yanzu ai ka bare su.
Sai da na tsame naman,
Amshi: Ga shi ai ka jigata.
Na ci na kasa tashi,
Amshi: Baba zari gareka.
Wannan waka tana fadakarwa ne a kan illar hadama da zari da kwadayi. Haka nan, wakar tana nuni a kan cewa, mutum ya ci gwargwadon bukatar cikinsa don gudun illa. A yayin aiwatar da wannan wasa, yara sukan zavi daya daga cikinsu ya yi shiga irin ta tsoho, sannan ya kifa kwarya ko ya sanya tsummokara a cikinsa don nuna yadda ya yi zarin cin abinci har ya cika masa ciki ya kasa tashi.
c.
Wayyo Allah,
Amshi: Ba mu kudinmu.
Kudinku na mene?
Amshi: Kudin doyarmu.
Ina Shaidarku?
Amshi: Mu je gun Inna.
Ku tsaya in ba ku,
Amshi: Ba mu kudinmu.
Ni fa dan gata ne,
Amshi: Me ke gatanka?
Wannan wakar tashe tana fadakarwa kan muhimmancin biyan bashi domin gudun mummunan wulakanci. Hakanan wakar tana fadakarwa kan kafa shaidu a yayin bayar da bashi don gudun rikici. A yayin aiwatar da wannan wasa, yaro daya ne zai shiga gaba, su kuma ragowar suna biye da shi sun rirrike rigarsa, shi kuma yana musanta da’awar kudin da suke bin sa.
d.
Ya Bismillah Rabbana,
Amshi: Jatau.
Za ni bayanin magani,
Amshi: Jatau.
In ba ku bayani dan kadan,
Amshi: Jatau.
Dawa ma na magani ko don yunwa ma a cira,
Amshi: Jatau.
Sabara na magani a tambayi mai jego a ji,
Amshi: Jatau.
Sanya ma na magani,ko don maye ma a cira,
Amshi: Jatau.
Ku jiyo marke na magani, ko don tari ma a cira,
Amshi: Jatau.
Allah ne mai magani,
Ko gunsa ka dage ya isa,
Amshi: Jatau.
Wannan waka da farko tana fadakarwa ta hanyar wayar da kai a kan ire-iren tsirrai da ‘ya’yan itatuwa masu maganin cututtuka. Hakanan, wakar ta fadakar cewa, babu wani mahaluki da yake da tasiri a kan komai in ba Allah ba. Bayan nan, wakar ta fito da wasu al’adu da wani rukuni na addini(dogaro ga Allah) da sana’o’in Hausawa.
Haka kuma, a lokacin aiwatar da wannan wasa, yara suna tanadar kwando sannan su nemi ’yan itatuwa da ganyayyaki da saiwoyi su zuba a ciki. Daga nan sai a sami wani daga cikinsu ya yi shigar mai bayar da magani, yana dagawa daya bayan daya yana fadar muhimmancinsu, su kuma sauran yaran suna amsawa.
e.
Ragadada,
Amshi: Ta hana ki riga.
danwake,
Amshi: Ya hana ki zani,
Shasshaka,
Amshi: Ta hana ki dankwali.
Soye ma,
Amshi: Ya hana ki takalmi.
Ragadada,
Amshi: Ta hana ki riga.
Wannan wakar tana fadakarwa a kan wasu munanan halaye kamar kwalama da kwadayi. Haka kuma, wakar tana fadakarwa a kan kishin zuci da neman abin kai da tattali da adana shi. Har wa yau, wakar tana fadakarwa kan saye-sayen da ba shi da amfani wadanda daga karshe, ko suturar kirki mutum sai ya rasa.
A wannan wasa, yara sukan sami wani ya sa kaya yagaggu, kuma masu dauda domin nuna rashin isasshiyar sutura saboda saye-sayen da ba su dace ba.
f.
Ga Mairama ga Daudu,
Amshi: Ga Mairama ga Daudu
Don Allah dauko Mairama,
Amshi: Ga Mairama ga Daudu.
Don Allah ki ba shi tuwo ya ci,
Amshi: Ga Mairama ga Daudu.
Don Allah ki ba shi ruwa ya sha,
Amshi: Ga Mairama ga Daudu.
Sai kin yi rausaya da ki ba shi,
Amshi: Ga Mairama ga Daudu.
Don Allah ki ba shi ruwa ya sha,
Amshi: Ga Mairama ga Daudu.
Sai kin yi rangwada da ki ba shi,
Amshi: Ga Mairama ga Daudu.
Wannan wakar tashe ta “Ga Mairama ga Daudu” tana fadakarwa ne kan yadda ya kamata mace ta yi wa mijinta, wato wakar tana bayar da tarbiyya ga ‘yan mata dangane da hakkokin miji a kan matarsa, sannan kuma ga bayyana muhimmancin aure ga jama’ar Hausawa.
A yayin wannan wasa, yara mata sukan tanadi irin ‘yan kayayyakin da ake kai amarya da su. Akwai kwanuka da tabarma da matasai da mafici da sauransu. Haka kuma, suna kwatanta yadda mace ya kamata ta yi wa mijinta idan ya dawo gida, wato tarairayar miji.
A dunkule, wadannan wakokin tashe suna kunshe da fadakarwa ga al’umma ta fuskoki daban-daban.
Ku kasance damu a babi na 2 don jin JIGON BAN-DARIYA CIKIN WAKOKIN TASHE
Tijjani Shehu
Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya,Jami’ar Bayero, Kano.