Get real time updates directly on you device, subscribe now.
ALBASA GA MACE KO NAMIJI
1–Albasa tana tacewa jinin jikin ‘Dan Adam. Duk mutumin da yake fama da matsalar karancin jini, ya yawaita cin albasa. insha Allahu jininsa zai yawaita.
2–Wanda yake fama da ciwon SICKLE (CELL ANEMIA) ya rika yanka albasa tare da Ganyen Zogale yana ci. Insha Allahu wannan ciwon Sickler din zai yi sauki
3—na uku kuma wanda yake shan wahala wajen yin fitsari ko bahaya, ya nemi Man albasa ya gauraya da zuma da lemon tsami. ya rika sha safe da yamma. kuma ya rika shafa man albasa ajikin Mararsa shima insha Allahu zai samu waraka cikin lokaci kankani.
4–sai kuma ciwon sugar Duk mai fama da yawan fitar fitsari saboda diabetes (Ciwon Sugar) ya nemi albasa mai kyau ya rika yankawa kullum yana ci.Insha Allah sugansa zai sauka, kuma zai dena yawan fita fitsarin
5–mata masu zubewar gashi duk matar da take fama da zubar gashi ko kwarkwata ko amosani ta samu man albasa da Man ridi da kuma garin Baqadunas ta kwaba ta rika shafawa a matsirar gashinta kullum kafin ta kwanta barci da safe sai ta wanke da ruwan zafi ta ci gaba da yin haka har tsawon kwana bakwai
6–daga karshe me ciwon basir ana yanyanka albasa a dafata sannan ayi kwadonta da kuli (karago) arinka ci kullum insha allahu za ayi mamaki