ACIGABA DA TARIHIN SARAUTAR ZAZZAU
A KASHI NA DAYA MUNTSAYA A
A kusa da Karni na 18th, Masarautar Zazzau ta rufe yanki waje 37,850 Sq MLs. Saboda haka, yana da muhimmanci mai karatu ya san cewa a ciki wannan lokaci, babban birnin mulkin ya canja daga Turunku zuwa Kufena (Dutsen kufta za’a iya ganin sa daga gidan sarauta).
ZAMU DORA
Saboda dogon zangon Habe wanda suka zo a kusan karni na 19th saboda mamayar Fulani tun a 1804.
Biyo Bayan nasarar Malamin addinin Islama Wato Danfodio cikin 1804, wasu malaman Fulani masu daraja sun karbi tuta Wato alama (alamar iko ko izinin) don gudanar da mulki a wuraren da suke.
Mallam Musa (Wanda ya kafa daular Malawa a Zazzau) wanda ya zama mai riqe da tuta a Zaria, kuma ya kasance tare da Mallam Yamusa (wanda ya kafa daular Bare-Bare a Zazzau) da Malam Abdukarimu (wanda ya kafa daular Katsinawa a Zazzau) a kan umarnin Danfodio. na zuwansa Zaria, wanda wakilan sukayi ƙoƙarin shiga cikin birnin ta Kofar Doka, lokacin da wannan ya zama mai wahala, sai suka hakura suka shiga ta Kofar Bai, wannan taron ya nuna alama mai tabatar da tarihin Zazzau.
Zazzau wata matatara ce ta Tara bayi don turasu zuwa kasuwanni na arewacin Kano da Katsina, inda ake canza su bayin da gishiri tare da dibansu zuwa kasuwa ta arewacin Sahara.
A cewar tarihi, a kwai addinin Islama a masarautar tun kusan 1456, amma ya bayyana cewa sun yadu sannu a hankali, kuma al’amuran bautar gumaka sun ci gaba har lokacin da Fulani suka ci nasarar a 1808. A lokuta da dama a cikin tarihin, garin Zazzau ya zama kamar na makwabatan jihohi kamar su Songhai, Bornu da Kwararafa.
Alhamdulillah
Karanta:
Tarihin Masarautar Zazzau Na 1