TARIHIN SAURANIYAR ZAZZAU AMINA KASHI NA DAYA

0 454

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sarauniyar Zazzau wato Amina, ta rayu daga shekarar 1533 zuwa 1610, ɗaya ce daga cikin ‘ya’ya biyu da sarkin Zazzau Bakwa Turunku ya haifa.

Wato ita Amina ɗin da kuma ƙanwarta mai suna Zariya. Ta yi sarautar Zazzau bayan rasuwar mahaifinta, daga shekara ta 1509 zuwa 1522, wato shekarunta 13 ke nan akan karagar mulki.

Kuma ita ce mace ta farko da ta mulki masarautar Zazzau, kuma ta shida a cikin sarakunan haɓe waɗanda sukai mulki bayan Addinin Musulunci ya fara bayyana a ƙasar Zazzau. Har ila yau a cikin jerin sarakunan Zazzau gaba ɗaya ita ce ta 23.

Sarauniya Amina ta shahara matuƙa a ƙasar Hausa da ma yankunan da daular Usmaniyya ta mulka.

Ta yi kaiwa da komowa na yaƙe-yaƙe a wurare da dama. Idan aka ɗauki tun daga Zariya har zuwa ƙasar Abuja akwai ƙananan garuwa da dama da sarauniya Amina ta kafa, sai dai ba masu girma ba ne, saboda kamar dai wurare ne da ta ci zango a wajen.

Da yake Kasar hausa na cikin yamutsin yake-yake tun daga wajajen shekara ta 1200 har zuwa 1700, Kasar zazzau ta zamo cikin halin rashin zaman lafiya da makwabtanta a wannan lokaci.

Daular Songhai ta kawo mamaya kasar hausa a wannan tsakani, garuruwan kano, katsina da Bornu kuma sun zamo manyan abokan gaba ga zazzau. Don haka akace kasar zazzau ta zamo tana matukar bukatar jarumin shugaba a koda wanne lokaci. Akan haka ne Amina ta gaji sarauta.

Muhadu a kashi NA biyu

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »