Amfanin Garin Kwallon Dabino

0 559

Ku daina jefar da kwallon dabino idan kun cinye dabinon, saboda yana da matukar amfani sosai a lafiyar mu, ga kadan daga cikin abinda akeyi da shi nan:

Ana yin Coffee da garin kwallon, sai a rika shan shayi da shi a matsayin MILO ko makamancinsa bal ma ya fi Milo amfani a jiki k kuma yana dauke da ingantaccen kamshi mai dadin shake.

Yadda ake iya zamar da kwallon dabino gari shi ne kamar haka:

Za ka samo kwallayen Dabinon ne sa ka wanke su sosai da kyau, katabbarar da komai ya fita a jikinsu kuma sun wanku da kyau, sai a tsane su su bushe a tabbatar da babu wata lema a jikinsu, sai a soya su a akan kasko tsawon mintuna 15 zuwa 20 ya danganta da yawansu, sai a dauko su a sa su a grander ko kuma wani abin daka sai a dake su suyi laushi sosai.

Yanzu sun zama Coffee, sai a rika shan shi da madara domin yana da matukar amfani sosai ga masu fama da matsaloli kamar haka:

1- Yana magance Matsalar cutar Sugar ta Diabetics type 1 ko type 2 da YARDAR ALLAH.

2-  Yana maganin matsalar ciwon zuciya da YARDAR ALLAH.

3- Yana baiwa Qoda da Hanta garkuwa da lafiya cikin YARDAR ALLAH.

4- Yana karawa fatar jikin mutum lafiya da YARDAR ALLAH.

5- Yana maganin matsalar tsinkewa ko zubar gashi da YARDAR ALLAH.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba. (Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSa)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »