Idan ka samo ruwan zafi kimanin Kofi 1 ka sanya zuma babban cokali 1 a cikin ruwan zafin, bayan ka juya shi sai ka shanye gaba daya da safe kafin kayi karin kumallo (Breakfast).
Yin hakan yana da matukar amfani ga lafiyar mu sosai kadan daga ciki su ne kamar haka:
1- Yana magance matsalar Makogwaro/makoshi da yardar Allah.
2- Yana magance matsalar Tari da matsalar sanyin dake jikin mutum musamman ma a kirji da yardar Allah.
3- Yana karawa zuciya lafiya da Yardar Allah.
4- Yana rage Qiba da tumbi da Yardar Allah.
5- Yana rage kitsen dake jikin mutum da Yardar Allah.
6- Yana gyara matsalolin dake tattare da hanjin cikin mutum da yardar Allah.
7- Yana narkar da majinar dake dauke da bacteria ko kwayar cuta da yardar Allah.
8- Yana inganta lafiyar zirga-zirgar jini da yardar Allah.
9- Shan ruwan dumi tare da zuma yana gyara fata yasa fatar mutum tayi kyau sosai.
10- Idan aka kara da lemon tsami Yana matukar kawar da kitsen dake jikin hanta, kuma yana da matuka amfani ga masu fama da ciwon Hepatitis A/B da C.
“Wannan kadan kenan daga cikin amfanin shan zuma da ruwan zafi, idan kacigaba da amfani da haka kullum da safe kafin kaci abinci za kaga wani amfanin a tattare da jikinka wanda ma ban ambaceshi anan ba da Yardar Allah.”
Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.
Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.
(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)
Domin karin bayani:
👇👇👇
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com