Wasu Daga Cikin Illar Kambun Baka

0 846

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

DAGA CIKIN ILLAR KAMBUN-BAKA

Duk wani Kambun-baka ko Kambun-Ido za ka sameshi da wani Shedanin aljani, shi wannan Shedanin aljanin yana rayuwa ne a kirjin mutane ( inda Zuciya take) da kafadunsu, idan mai Kambun-baka ya shafi mutum sai kaga Shedanin aljanin nan ya kara tabbata a jikin mutum tayadda zai rika bin dukkanin wasu hanyoyin jini da suke a jikin dan Adam, sai kaga mutum yana fama da matsalolin cututtukan da suka shafi jini kamar: Blood Cancer, Diabetics, Hawan jini, Sikila, Anemia da suaransu.

Kuma yana shiga har cikin ciki wajan kayan ciki musamman ma cikin hanji da uwar hanji, sai kaji mutum yana jin wasu cututtukan da suka shafi kayan ciki musamman ma Hanji kamar : Ulcer, da tsananin ciwon ciki da sauransu. Yawancin cututtukan nan ba wai sai kaga anje asibiti amma sai aga ba komai, ayita magani amma ba komai, to da zarar an fahimci hakan ba makawa wannan yana da alaqa ne da Kambun-baka ko Kambun-Ido.

MAFITA

Mutum yadukufa da Azkaar, idna zinari fita gida yayi Azkaar, karatun Alqur’ani ba dare ba rana, boye sirri, rufe jiki da rufe tsiraici da kuma wanke hannu da yin Addu’a yayin fara cin abinci.

1- Mutum yasamo Man Habbatus saudah mai kyau sosai, ya karanta Alqur’ani a ciki musamman wadan nan Ayoyin : Fatiha x7, Ayatul Kursiyyu x7, Karshen Baqara x7, Ikhlas x7, Falaqi x7, Nasi x7, sai ya rika shan cokali 1 na man kullum da Asubah kafin yaci komai. (Wannan ga mai fama da matsalar da ta shafi jini kenan wanda ke da alaqa da Kambun-baka).

2- Mutum ya zuba zuma mai kyau adadin cokali 5 ko 7 a cikin kofi daya na ruwan sanyi ordinary ba mai sanyi ba kuma ba mai dumi ba, sai ya karanta Alqur’ani musamman wadan nan : Fatiha x7, Ayatul Kursiyyu x7, Karshen Baqara x7, Ikhlas x7, Falaqi x7, Nasi x7, a cikin ruwan ya motsa yasha da safe da yamma ma yakarayi yasha har tsawon kwanaki 3 zuwa 5 ( Ga masu fama da matsalar da ta shafi matsalar ciki kenan wanda ke da alaqa da Kambun-baka).

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu’aym)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »