Wasu Daga Cikin Almomin Sihiri Mafi Hatsari Ga Mace Mai Aure.

0 624

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

DAGA CIKIN SIHIRI MAFI HATSARI

Sihirin dayake kama mahaifar mace yana daga cikin nau’ukan Sihiri masu matuƙar hatsari, saboda sihirin yana aiki ne a iya mahaifar mace mai aure, kuma yawancin irin sihirin nan asalinsa Sihirin raba tsakanin MA’AURATA ne ko kuma sihirin DAN BAKA 🏹 ( wanda kishiya take yiwa abokiyar zamanta sai miji yakasance ba ya iya biyawa dayar bukatar ta tazama saniyar ware).

Kuma shi sihirin da yake kama mahaifar mace yana iya sabbaba hana ɗaukar ciki, yana sabbaba yawan zubewar ciki kuma yana sabbaba ma’aurata su daina jin dadin mu’amala da junansu, amma duk sai da IZININ ALLAH.

Sai kaga mara lafiyar sunje asibiti ayita gwaje-gwaje amma a rasa gano abinda ke damunsa, duk wannan sharrin SIHIRI ne mai kama mahaifa ta yadda duk wani tsafin matsafi bazai taba yin tasiri ba sai DA IZININ ALLAH.

ALAMOMINSA :

Jin ciwon kai mai tsanani kuma yana karuwa ne a lokacin da maigida ya shigo gidan, jin ciwo mai tsanani a kasan baya, Jin kunci a zuciya, jinkirin zuwan Al’ada, Jin zafi yayin saduwar aure, da sauransu.

MAFITA :

A samu MISKIL KA’ABA ko BAKIN MISK ko kuma JAN MISK a karanta Alqur’ani a cikinsa sai a rika shafawa a mara da kuma baya setin mahaifa kullum da daddare, sai kuma a samu man zaitun a karanta masa Alqur’ani aciki sai a rika shan cokali 1 safe da rana da dare kullum kuma ana shafawa a jiki.

Insha ALLAH za aga sauyi cikin hikimar ALLAH.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Dan uwanku:
Idris M Rismawy (Abu Nu’aym)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »