Yadda Za’a Magance Rashin Ruwa Mama Ga Masu Sha Yarwa.

0 370

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

1- A samu RIDI a tsaftace shi sosai sai a hada shi da MAN SHANU da GARIN HULBA da kuma ZUMA a kwaba su sai mace ta rika sha akai akai, in Sha ALLAHu wannan hadin yana sabbaba Allah yasamar da ruwan nono mai kyau mai dauke da sinadaran da suke karawa yaro lafiya da kuzari cikin yardar ALLAH.

2- A samu RIDI sai ayi garin shi a kwaba shi da MAN SHANU sai a rika shafawa a nonon in Sha ALLAHu ruwan nono zai samu da yaradar ALLAH, Wadannan mujarrabi ne.

A hada su gaba daya 1-2 ayi amfani da su na sha din da an shafawa … Allah yataimaka.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »