Sanadin So ( Kashi na 4 Hausa Novel )

0 130

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

SANADIN SO KASHI  HUDU

Kai tsaye kwamanda ya nemi kujera yazauna. ci gaba da maganarsa, ban yi tunanin zaka shigo hannuna da wuri haka
ba, koda yake kuma ba abin mamaki ba ne domin kuwa Hausawa sun ce quda wurin kwadayi ake mutuwa, to kai a qudan ma ka zarta kowa a kwadayi.

Na rasa gano me ke damunku ‘ya’yan talakawan nan ba zaku iya tsayawa a matsayinku ba ku nemi ‘ya’yan talakawa tsaranku, sai kullum ku ne like da kyawawan mata, matan da aka yi don masu hannu da shuni in ban da wauta irin taku talakawae zai kai ku wurin.

Ba sai na tambayeka ba dan samari ga mamaki nan karara a fuskarka, na san kana mamaki ne jin na ce maka fateema matata ce, a farko kuma na ce maka ‘yata ce ban maka karya ba dan samari a tarin shekaru na haifi fateema, sai dai a zamantakewa ta aure matata ce, na san ba yanda za’a yi ta sanar da kai tana da aure ahi yasa nima na ce da kai ni ne mahaifinta saboda na san zaka fi saurin shigowa hannu, yanayin wahalar da nake ciki bai hanani gano dogon mutumin dake tsaye gabana mai wakiltar sunan kwamanda,,,, Allah yayi masa baiwar tarin surutu kamar waziri Aku ba.

Ba tare da la’akari da me zan ce ba ya sake dorawa, babu abinda nake so a duniyar nan kamar matata fateema, idan kuma akwai abinda na tsana a duniyar nan to abinda zai rabani da ita ne. gashi kai kana kokarin ka kwaceta daga gareni. Don girman Allah kayi hakuri, Wallahi ban san.matarka ba ce, hasalima ban san tana da.aure ba Wallahi da ko kusa ba zan nemeta ba.

Na tari numfashinsa ina masa magiya. Murmushi Mugunta yayi min, sannan ya sake ci gaba da maganarsa kwantar da hankalinka ai na san baka san matata ba ce da ba zaka yi gangancin zuwa gidan nan ba domin rijiya ba wurin wasar makaho ba ne.


Sai dai rashin sa’a daya kayi, ba na iya yafewa duk wanda ya ra6i fateema da sunan so, to kai gashi har soyayyar kuke yi. Lokaci daya kuma sai ya turbune fuska kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwar Fateema, sannan ya kira Samudawan nan da suka jibgeni dazu..Ku mikaminshi wurin M.P (Military Police) a yi masa horo mai tsanani har sai na waiwayeshi.


Hankalina in yayi dubu a lokacin sai da ya tashi jin Kwamanda ya bada umarnin a kai ni wurin masu ladaftar da sojoji idan suka yi laifi wato Military Police, ihu na shiga yi ina masa. magiya a kan yayi hakuri amma kamar baya jina. Wasa farin girki dukan da na sha a baya ba ko duka ba ne yanzu zan fara shan azaba Cakumata suka yi kamar tsumma suka yi waje, muna tafe ina sake-sake a raina ko.shakka babu da za’a yi nadin sarkin wawaye to babu wanda ya dace a nada sai ni.


Yaya daga haduwa da yarinya WhatsApp. muna soyayya ban taba ganinta a zahiri ba haka ita ma bata taba ganina a zahiri ba sai. dai a hoto, kawai wani ya kirani a waya wai mahaifinta ne yana son ganina sai kawai in tashi in tafi, in ma har da gaske ne ai ita ya kamata ta sanar dani sakon na mahaifinta ba wai shi ya kirani ba, a gefe daya kuma ina tunanin irin azabar da zan sha a hannun M.P.


maganar wani abokina da ya taba zuwa. tirenin din soja ta fadomin wai ko soja yayi laifi yana tsoron M.P su kamashi soboda.azabar da zai sha a hannunsu. soja kenan, to ina ga ni farar hula, a farar hular ma zan fi dacewa da a kirani da mace mai tsohon ciki wata tara, a kan a kirani namiji saboda ragwancina.

Da wadannan sake-saken muka isa suka hannuntani a hannunsu suka kama gabansu. Tashin hankali ba’a sa maka rana kwanana biyu cur a hannun M.P suna ganamim azaba har sai da na rika tunanin anya ba mutuwa ne nayi ba, a lahira ne nake shan wannan. azabar, saboda kwata- kwata azabar bata yi kama da ta matambayan duniya ba.

A washe garin kwana na uku kwamanda ya bada umarni a sakeni bayan ya gargadeni a. kan ko mai sunan farida na kara kulawa na san sauran.. Satina uku cur a gida ina jinyar raunukan da M.P suka yimin ko kofar gida bana iya fita. ina kwance ina jinya na toshe duk wata kafa da nake ganin zan iya tuna fateema nayi blocking dinta a facebook da WhatsApp, na goge lambobin wayarta da duk wasu hotuna da ta turomin nata. ina ganin mun yi bankwana kenan har abada, ashe wai da sauran rina a kaba.


Bayan kamar wata daya da gama jinyata, ina zaune shago bisa keken dinkina na dukufa sai dinki nake wata madaidaiciyar mota launin ruwan siminti ta yada zango bakin kofar shagon dinkin, wani abokina ya taba fadamin sunan motar wai ko Continue Discussion ne sunanta.

Irinta ne mijin kanwana AISHA yake shiga Gabana ba karamar faduwa yayi ba lokacin da naga wata matashiyar budurwa ta fito daga motar kai tsaye ta kunno kai cikin shagon doguwa ce sai dai ba sosai ba tana da matsakaiciyar fuska mai dan tsawo dauke da dara-daran idanu da matsakaicin baki tana da saje a fuskarta launin fatarta kuwa. wankan tarwada ce, shekarunta zasu iya kaiwa ashirin da uku zuwa da biyar, kallo.daya nayi mata na shaidata kasancewar na saba ganin hotunanta.

Fateema ce. me kuma ta zo yi a shagona? tambayar da.nayi wa kaina kenan…!


MUTANENA zamu ci gaba gobe a part 5 insha Allahu.


ME RA’AYINKU AKAN WANNAN LABARIN ???

Ab Kudancy

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »