Bani Da Lafiya Kashi Na Tamanin Da Daya (81)

0 573

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Miskil Ka’aba shima daya ne daga cikin nau’ukan Misk kamar ( Jan misk da bakin Misk) wanda shi na Ka’aba yana da matukar tasiri ga matsalar Jinnul Aashiq musamman ma Aashiq din da suke zaune a mahaifar mace.”

Mai gabatarwa yace: Wato Malama idan na fahimta kenan kina nufin: MAN ZAITUN da na HABBATUS SAUDAH ne dabam za a hade su wuri guda a karanta musu wadannna Ayoyin ko?

Kuma shi na Misk Ja ko Baki ko kuma na Ka’aba shi ma dabam za a karanta masa waɗannan Ayoyin kenan ba hadesu za ayi da zaitun din ba ko?

Malama : Kwarai kuwa haka nake nufi, kuma ALLAH yasa ma sauran mutane masu sauraro sun fahimta.

Sai kowa a dakin taron aka amsa da cewa: Na’am Malama duk mun fahimta, Allah yabada lada.

Malama taci gaba da cewa: Bayan an kammala karatun a cikin Misk din sai mai ciki ta rika shafawa a cibiyarta da cikinta da mara da kuma bayanta setin inda mahaifarta take.

Sannan kuma shi wannan Man Zaitun da na Habbatus saudah din mace mai ciki za ta rika shan cokali daya ne a lokacin da cikin ya girma yakai watanni 7 zuwa ranar haihuwa kuma hakan yana sanya hauhuwa tazo da sauki cikin hikimar ALLAH.

Kuma yana da kyau ga mai ciki ta tanadi ruwan shanta yakasance ta karanta masa wadannan ayoyin a cikin ruwan sai ta zamar da shi ruwan shan ta a ko da yaushe.

Lokacin Sallah yayi sai aka dakatar da komai domin aje ayi sallah sai kuma a dawo acigaba da muhadarar…

Bayan kowa ya fita waje ne, sai Maman Sultan taga mutane suna ta fitowa daga cikin dakin taro, sai ta tambayi wata mata tana cewa: Baiwar Allah, don Allah me akeyine anan naga kowa na shiga da yan makaranta da ma wadanda ba yan makarantar ba kuma ba ranar makaranta ba?

Sai matar tace: Wallahi muhadara akeyi ne mai matukar kayatarwa sosai akan Illar mu’amala da bokaye da kuma zuwa wuraren gurbatattun malamai masu duba da yan tsubbu da sauransu, kuma sai aka nuna mana abubuwan da suka halasta a shari’ar Muslunci ayi domin samun kariyar ALLAH daga dukkanin sharrin halittunsa.

Maman Sultan ranta ya ɓaci sosai, ta murtuke fuska, sai can ta hango tawagar su Labeeba da Bareerah za su je masallaci nan take kuwa sai cewa matar tayi: Na ji don Allah dakata haka, je ki kawai na gode ( cikin fushi tana hantarar ta).

Bayan tafiyar matar ne sai Maman Sultan tana magana a cikin zuciyarta tana cewa: Tab dijam, ai tunda naga wadannan yaran nasan ba alheri za a kulla mana a makarantar nan ba, kasuwar mu kawai za su kashe mana.

(Allah ya kyauta insha ALLAH za muji ci gaban bayanin a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »