Masu Matsalar Wasuwasi Ga mafita Da Izinin Allah.

0 257

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

1- Ka samo garin Qustul Hindi ƙaramin cokali 1 ka sanya shi a ruwa kofi 1, sai ka garwaya shi ya garwayu sosai, sai ka karanta masa Ayoyin Alqur’ani Kamar su “Fatiha, Ayatul Kursiyyu, Ikhals, Falaqi da Nasi” , sai ka riqa sha kuma kana shaqawa a hancin Ka (irin shaqa ruwan da kakeyi a alwala).

2- Ka rika karanta wannan Addu’ar sau 7 da safe da yamma ma sau 7:
“حسبي الله لا إله إلا هو عليه توكلت وهو رب العرش العظيم.”

“HASBIYALLAHU LA ILAAHA ILLA HUWA ALAIHI TAWAKKALTU WA HUWA RABBIL ARSHIL AZEEM.”

  • Yawaita yin ISTIGFAARI a ko da yaushe ba tare da qayyade adadin da zaka yi ba.
  • Karanta AYATUL KURSIYYU a bayan kowace sallar farillla da lokacin da za kayi bacci.
  • Yawaita karanta Alqur’ani a hali ko yanayin da shari’a ta amince.
  • Karanta suratul Baqara da suararonta a kullum ko da baka karance ta dukkanta ba.
  • Yin alwala a kullum idan zaka kwanta bacci, ko da ma’aurata sun sadu da junansu basu samu damar yin wanka da daren ba, su samu suyi alwala ko da sabi 1 ne ba sai sabi 3 ba.
  • Idan kazo alwala kadaina yin almubazzaranci da ruwan, ka riga dibar iya wanda zaka iya amfani da shi.
  • Adaina sauraron kade kade da wake wake.
  • A rika yawaita sauraron Alqur’ani.
  • Karanta Suratul Ikhlasi, falaqi da Nasi sau uku safe da yamma, da sauran Azkaar na safe da yamma.
  • A rika shiga cikin jama’a, mutum ya daina kebewa shi kadai.

Kuma idan anga sauyi kar a daina yin azkaar din, acigaba da yinsu.
Insha ALLAHu za ku daina yin waswasin cikin iko da yardar Allah.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »