Bani Da Lafiya Kashi Na Sittin Da Daya Babbanci Tsakanin Boka Da Malami

0 5,048

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Bareerah : Wadan nan ai ba boyayyu bane, su ne kamar haka:

1-MASIHIRCI ko MATSAFI :wanda ke yiwa mutane ko a sanyashi yayi sihiri ko tsafi ya raba tsakanin ma’aurata mata da mijinta, iyaye da yayansu, ko yacutar da mutane ko kuma ya amfanar da su ( kamar yadda suke cewa), irinsu sun hada da mayu, matsafa da yan kungiyar asiri da sauransu.

2- BOKA : Mai nuna ya san wani boyayyen abinda zai faru a nan gaba saboda yana aikine da wasu shedanun Aljanun da suke labarta masa abinda zai iya faruwa a nan gaba ( Na daga abinda suke tsinkayowa daga cikin tattaunawar da MALA’IKU ke yi a tskaninsu,) amma suna surkawa da karairayi da yawa saboda yawancinsu duk makaryata ne.

3- DAN DUBA: Mai duba abinda yafaru a baya, anyi maka sata sai ya duba yaga wanda yayi satar, ko kayanka sun bace sai ya nuna inda kayan suke, kamar masu bugun kasa da masu aiki da taurari domin gano abinda ya buya. Allah ya kyauta.

“Amma BOKA zai iya zama MASIHIRCI kuma MASIHIRCI zai iya zama BOKA saboda dabi’un nan 2 za su iya kasancewa tare a wurin mutum daya, amma bambancinsu shi ne: Shi masihirci da Dan-duba ba zasu taba yi maka magana akan abinda zai iya faruwa da kai anjima, gobe ko nan gaba ba ( saboda ba su da shedanun Aljamun da suke labarta musu hakan) BOKA ne kawai ke da damar yin haka saboda shi ne kadai ke amfani da shedanun Aljanun da suke iya bayar da labarin abinda zai faru a gaba. Kamar yadda Al- Allaamah Ibn Uthymeen yafadi ( Allah yayi masa rahama).”

Matar dai tayi shiru tana sauraro sai can tace: To amma Yar uwa a cikinsu wanne ne wanda Addinin muslunci ya nuna ko ya amince muje wurinsa Neman Magani a cikin su ukun nan?

(Insha Allahu za muji abinda ke gaba a rubutu nagaba)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »