“Duk tsawon shekarun da kika dauka bakiyi aure ba karki yarda kiyi asarar Imaninki da kudadenki wajan biye-biyen bokaye da malaman tsubbu saboda kawai kina so kiyi aure, kisani cewa duk abinda kikaga ya faru to lokacinsa ne yayi, wanda bai faru ba ma lokacinsa ne baiyi ba, kuma indai har Allah ya tabbatar za kiyi auren to za kiyi ne komai daren dadewa. Hakuri da addu’a tare da yiwa Allah biyayya da kyautata masa zato su ne fitilun da za su rika haskaka miki hanyar rayuwa har ki dace, amma ba wai boka ko mallam ba.” Kai tsaye matar ta karasa wurin su Labeeba, tayi musu sallama suka amsa. Ita Labeeba ta gane matar sai ta dage niqab dinta don matar taga fuskarta da kyau, sai kuwa tana ta mamaki har take cewa: ” Ina ganin kamar ke ce muka shigo taxi tare da ke ko?” Labeeba: Eh, nice tare da maman Sultan ko? Matar: Kwarai kuwa, ashe ma kinsanta kenan? Labeeba: Kwarai kuwa ai na gane ta tun a cikin taxi din, itace dai bata ganeni ba, saboda niqab din da na sanya ne. Bareerah: Wai kina nufin Maman Sultan dai wacce na sani? Labeeba: Kwarai kuwa itafa. Amma ke baiwar Allah me ya hadaku ne da ita? Labeeba ke tambayar matar. Matar tayi murmushi tace: doguwar maganace, amma dai mu koma wani wuri mu zauna sai mu tattauna da kyau. Labeeba : Ba matsala, mu karasa can wurin na ga kamar ba kowa, Bareerah kema zo muje tare saboda wani taimako ne zamuyi. Bayan sun zauna ne sai Breerah take cewa matar: Wai amma menene ma yahadaki da Maman sultan ne haka har kuka fara maganar bokaye da ita? Matar : Wallahy ingaya miki wata yar Uwata ce muka rasa abinda ke damunta game da aure, saboda ta kusan shekara 40 amma shiru har yanzu ba tsayayye kowa yazo sau daya bazai kara zuwa ba, shine ita Maman Sultan din take cemin akwai yadda za ayi, shine muka fara maganar da ita a cikin taxi har kuma taqaddama ta faru tsakaninta da su wannan baiwar Allah din. Labeeba: Subhanallah ! Allah ya kyauta, Allah dai yasa iya nan kuka tsaya bata kara tallata miki wata hajar bokayen ba. (Insha ALLAHU a rubutu nagaba za muji ci gaban lamarin.) Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba. (Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻) Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
ABIN LURA
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com
Get real time updates directly on you device, subscribe now.
Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com
Next Post
- Comments
- Facebook Comments