Amfanin Ganyen Kubewa / Kabushe Ga Lafiyar Jiki.

0 775

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ba wai iya Kabewar ce kadai abin amfani ba, hatta ganyenta ma yana da matukar amfani ga lafiyar mu kwarai da gaske. Sauran Kabilun kasar nan da ma na wasu kasashen Africa sun dade suna amfani da ganyen kabewa wajan yin miya da shi irin yadda muke yin miya da ganyen alayyaho ko ganyen Ugu.

Ganyen kabewa yana tace jini ya raba jini daga gurbacewa cikin yardar Allah.

Ana so masu ciki da masu shayarwa da masu fama da rashin karfi ko kuzarin jiki su rika cin miyar ganyen Kabewa.

Ana so masu matsalar hawan jini da ciwon diabetic, Cancer ( ta Mama ko ta jini) ko HIV su rika amfani da shi wajan matse ganyen (da duk abinda yakamata a matse) sai a rika shan ruwan. Insha ALLAHu akwai fa’ida kwarai da gaske.

ABIN LURA

A LURA DA KYAU…:

Jaririn ganyen ne wanda yake fitowa daga sama ake amfani da shi, ba wai manyan ganyen ba wadanda suka dade a jikin kabewar ba.

ALLAHu A’alam.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »