Bani Da Lafiya Kashi Na Hamsin Da Uku (53)

0 520

ABIN LURA

“Duk wani malami ko mai maganin da yace zai iya yin abinda Allah ne kadai zai iya yinsa, to ya zama wajibi ku kaurace masa saboda BOKA ne shi, in ba haka ba kuwa zai kai ku wuta, saboda makomar bokaye da duk wadanda ke zuwa wajansu itace Wuta matukar basu tuba ba kafin su mutu. Allah yakara tsare mana imaninmu.”

Labeeba tayi murmushi sai itama tace: Wallahi kuwa mallam, ai yanzu ma wasu matan sun zama yan aikin bokaye saboda har kasa musu talla bokayen keyi su rika samo musu kwastamomi. WaL iyadhu biLLAH !

Maman Sultan ta kama kallon Labeeba kallo mai dauke da harara da wulakanci, amma bata ganeta ba har yanzu sai cewa tayi: Uhunm, ashe dai maganar da mutane ke fadi gaskiya ce, tsabar munafurci ne kawai kaga mutum ya wani lullube fuskarsa kamar na Allah ashe dai duk munafukai ne ingaya miki.

Matar da suka taho da Maman Sultan, ita ta kasa gane kan bayanin da ake yi, sai ta kada baki tana cewa: Wai Maman Sultan me ke faruwa ne naga ana ta sakin maganganu haka ?

Maman Sultan taga dai idan taci gaba da zama a taxi din nan mutanen nan za su iya sanya matar nan ta gane abinda ake ciki, sai tacewa Direban: Akwai anan idan ka samu wuri za mu sauka.

Maman Sultan suka sauka a taxi din tana ta bakaken maganganu amma dai Labeeba bata tanka mata ba har suka kara gaba. Sai direban ke tambayar Labeeba yana cewa: Wai Hajiya kinsan matar nanne?

Labeeba: Kwarai kuwa, a makarantar mu take aikinta kenan mu’amala da bokaye shi yasa har yanzu ta kiyin Aure ta rufawa kanta asiri, kullum tana kan hanyar kai mutane gidajen bokaye tayi ta batar da su.

Direba: Allah Sarki, lallaikam wannan matar sai dai muce Allah ya shiryeta da duk masu irin halinta, mu kuma Allah yakara tsare mu da tsarewarSA, domin nima na santa sosai da wannan harkar saboda a unguwar mu suke, kowa ya santa da wannan bakar harkar ta mu’amala da bokaye don har duka aka kusan yi mata watannin baya da suka wuce saboda ta raba wata mata da mijinta suna zaman zamansu.

Labeeba: Ikon Allah kenan, to su kuma a garin yaya har suka biye mata aurensu ya rabu haka ?

(Insha ALLAHu za muji dalilin a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »