Bani Da Lafiya Kashi Na Arbain Da Uku

0 237

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ABIN LURA

“Muyi hakuri mu rika neman haihuwa ta hanyar da ta dace da shari’ar Allah, domin duk wanda yabi gurbatacciyar hanya har ya samu haihuwa to ya tabbata shi da zaman lafiya a rayuwarsa sunyi hannun riga kenan, domin wannan abinda ya haifa din zai zamar masa alaqaqai saboda ya zama ‘DAN ALLAH BA NI.”

Ummu Arqam: Subhanallah ! To fa ai ka ji irinta, na tabbata wannan mutanen sai sunbi hudubar shedan ya hallakar da su gaba daya.

Abu Ruwaihah: Ai kam kamar a gabanki lamarin yafaru, domin wajan wani boka suka je, shi kuma a karshe sai da yace: Za ta iya samun haihuwa amma dole sai ta amince ya kwanta da ita tukunna .

Abu Arqam: Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un..! Yanzu akan dukiya da neman haihuwa sai ta bari wani kazami yayi lalata da ita ? Ya ALLAH kakara tsare mana imaninmu.

Abu Ruwaihah: Ai Dan uwa kai dai rabu da mutumin da yake sun abu ido rufe, ba ruwanshi da kawo Allah ne kadai mai bayarwa, domin da farko itama kanta yarinyar jikinta ya yi sanyi, amma da ta fadawa mahaifiyarta yadda suka yi da bokan a maimakon ta hana ta ko ta nuna mata illar yin hakan sai kawai ta bata kwarin gwiwa, tun yarinyar tana ja baya har sai da tazo ta amince.

Abu Arqam: Subhanallah ! Ai ka ji irin hanyar da shedan ke amfani da bokaye wajan hallakar da al’umma suna ruguza Imaninsu da kansu. ALLAH yakara tsare mana imaninmu.

Ummu Arqam : Wato shi yasa fa ni na tsaya nake ta taka tsantsan akan lamarin nan, don dai kawai ALLAH bai haramta mana riko da sababi bane ( matukar bai sabawa tauhidinSA ba), amma kam da ba ruwa na da neman wani maganin nan.

Abu Ruwaihah: Ai kam dole sai da taka tsantsan saboda gudun afkawa cikin irin wannan matsalar.. ALLAH yakara tsare mana imaninmu.

Abu Arqam: To wai kuma sun samu haihuwar kuwa?

(Insha ALLAHu za muji ci gaban a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »