Yadda Zaa Mangance Zanen Fuska Duk Dadewarsa.

0 1,768

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Zanen fuska suna da yawa, kuma sukan sanya mutum yayi muni sosai. Amma yanzu babu damuwa, akwai mafita mai sauƙi don cire su. Kuna buƙatar minti 15 kawai a kullum kuma za ku ga sakamako ba da daɗewa ba.

ABINDA ZAKU NEMA:

• Man zaitun cokali daya

• Cokali daya na Aloe Vera Gel

• Garin Alkama/flawa Cokali ɗaya

HANYOYIN ANFANI DASHI:

Zaku Saka duk waɗannan abubuwan a cikin kwano ko kofi. Saiku juya su sosai har sai sun haɗu da kyau. Saiku deba ku sanya a inda tabon yake kuna ɗan murzawa a hankali.

Bayan kun gama saiku kyaleshi na tsawon mintuna sha Biyar (15) a wajen.

Bayan ya gama wanann mintuna saiku samu tawel mai kyau ku tsomashi a ruwan zafi saiku goge wannan abin dake fuskar ku dashi jiƙaƙen tawel ɗin.

Insha Allahu idan zakuyi haka kullum zaku nemi wannan tabon fuskar ku rasa. Allah ya bada Sa’a.

ABIN LURA:
Ruwan zafin da muka ambata a baya bawai mai zafi sosai ba dan dai-dai misali.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »