Bani Da Lafiya Kashi Na Tara (9)

0 588

Bareerah taji tausayin Labeeba ya kama ta sai cewa tayi: Allah Sarki yar uwa, wato nima din nan da kike gani na yi fama da matsalar Jinnul Aashiq din nan a baya, amma yanzu Alhamdulillah ba ni da matsalar ko kadan.

Labeeba : Ikon Allah kenan, wai dama ana warkewa daga wannan lalurar ne gaba daya?

Bareerah: Kwarai kuwa yar uwa, ai babu cutar da ba ta da magani kuma babu abinda zai iya gagarar Allah saboda SHI kadai ne mai bayar da waraka domin daga cututtukan da masu dauke da cutar har warakar duk bayinSA ne.

Labeeba: Tabbas kuwa, Allah gwani ne wanda ba shi da kama ko kadan, mu ma dai Allah yasa mudace mu rabu da ita.

Amma ke wace hanya ce kikabi kika samu taki warakar? Tambayar kenan da Labeeba tayiwa Bareerah domin ta samu karin haske.

Bareerah: Wato abinda nake ta kokarin fahimtar da wadancan kawayen nawa kenan, amma su hankalinsu ba ya wurin yana kan abinda Maman Sultan ke zayyana musu, kuma wallahy ba abinda take tsunduma su ciki sai halaka da tabewa.

Labeeba: Tabbas kuwa domin naji irin abinda kuke ta tattaunawa akai.

Bareerah: Ai ba ma tun yau muka fara irin haka da ita Maman Sultan ba, saboda a baya ta taba jefa wata yarinya cikin nadama akarshe yanzu yarinyar ta bar gida ta fita yawon duniya saboda takaicin ba zata iya zama a garin ba.

Bareerah taci gaba da cewa: ingaya miki Yarinyar an kusa yin aurenta saura sati 2 , kawai Maman Sultan ta yaudari yarinyar nan wai taje ayi mata istihara akan wanda za ta aura agani ko aurensa akwai alheri…

Labeeba: Ikon Allah, istihara kuma! Wannan wace irin istihara ce kuma haka?

Bareerah tace: Ai wato yanzu mutane sun mayar da Istihara wani abu can dabam ba yadda Addini ya koyar da ita ba, Kaicooo.

Labeeba: Ai kam dole a rika afkawa ga halaka saboda mutane sun bar tsarin Allah da abinda ManzonSA Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar da mu game da yadda ake yin istikharar, an kama shirme da shiririta wasu ma har shirka suke yi, Allah mun tuba.

Bareerah: Wallahy kam, ai ingaya miki yarinyar nan ba bu yadda banyi da ita ba akan cewa ta ajiye maganar wannan istiharar, ta cigaba da Addu’ar ALLAH ya sada ta da dukkanin alkhairan dake cikin wannan auren kuma ya kare ta daga dukkanin sharrin dake cikinsa, amma yarinyar nan kememe tayi watsi da magana ta.

Bareerah taci gaba da cewa: Ai kam suka je aka yi istiharar nan akace ai wanda za ta aura ba bu alheri a tattare da shi kawai ta fasa auren nan.

Labeeba: Subhanallah ! Ta fasa auren kuma bayan saura sati 2 ?

Bareerah: Hmm ai kuwa haka akayi, domin Maman Sultan haka tacewa yarinyar : Ai kam kar ma ki kuskura ki sanar da iyayenki cewa ga inda muka zo nan , kawai ki bijire kice ba kyaso kin fasa auren, ayi yin duniya ke ko ki kyekyeshe kasa kice bakisan zancen ba kawai kin fasa.

Ai kam yarinyar nan ta bi hudubar Maman Sultan, ta yi duk abinda ta umarce ta, dole iyayenta suka mayarwa da wancan kudinsa da kayan da ya kawo aka fasa auren.

Labeeba: Kaico…amma yarinyar nan akwai sokuwa wallahy, tab dijam yanzu yadda mazajen aure ke wahalar samu, ka samu wanda zai rufa maka asiri ya aureka ma ai ba karamin aiki bane, amma ita tayiwa nata haka hmmmm.

Bareerah: Hmmmm kenan dai kin fadi… kuma wallahy yarinyar ta jima ba ta da aure duk kanneta da kawayenta sunyi auren, sai yanzu ta samu amma kuma aka zuga ta ta barar da damar ta, yanzu ga shi ingaya miki yarinyar ba ta da wanda za ta aura, sai samarin banza kawai wadanda za su lalata mata rayuwa, shi kuma wanda ta kora din tuni yayi aurensa har da ya’ya 2, amma ita tana ta garararanba a gari.

(Insha ALLAHu za muji abinda ya faru a rubutu nagaba)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »