Shin Ko kunsan Cewa Sautari Shaidanu Nayin Sular sake-saken Aure

0 367

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ko kunsan cewa yawancin sake-saken auren da suke faruwa a yanzu ( bance duka ba), za ka tarar akwai hannun Shedanu dumu-dumu a cikin lamarin…!

Ko dai ya kasance ta hanyar WASWASIN SHEDANU kamar yadda yake a hadisin Jabir ( Allah yakara masa yarda) wanda yake cikin “Sahih Muslim” wanda shedan ke aika tawagarsa zuwa mutane, duk wanda yafi aiki a cikinsu shi ne wanda yazo yace : “Ban rabu da wane ba har sai da na raba tsakaninsa da matarsa.” Sai Shedan yakara masa girma saboda shi ne wanda yafi aiki a cikinsu.

Ko kuma yakasance ta hanyar SIHIRIN RABA TSAKANIN MA’AURATA, wannan ALLAH ya labarta mana game da burin MASIHIRTAn shi ne: Su raba tsakanin Miji da matarsa kamar yadda yazo a cikin Alqur’ani maigirma a Suratul Baqara (Aya ta 102) cikin labarin HAARUTA da MAARUTA. Amma duk ba za su iya yin haka ba a karankansu sai da IZININ ALLAH.

Ko kuma ta hanyar KAMBUN-BAKA wanda yake shiga tsakanin ma’aurata ta sanadiyyar rashin rike sirri da kuma yayata komai na ni’imar da take tsakanin su ga kowa, akarshe sai dai suga zamantakewrsu ta fara tsami sun fara tsanar junansu ko suna son su rabu da juna ba tare da wani dalili ba.

Ko kuma ta hanyar MASSUL AASHIQ/JINNUL AASHIQ wanda yake sanya mace ta rika tsanar mijinta har ta rika son rabuwa da shi ko kuma shi ma mijin yarika jin hakan kamar yadda take ji, kuma a baya kafin haka akwai gamsasshiyar soyayya a tsakaninsu.

SHAWARA

Ina mai shawartar yan uwa da mu dage wajan yin Addu’ar neman ALLAH ya bamu kariya daga sharrin halittunsa, wajan yawaita tuba da yin Azkaar na safe da yamma, da kuma karanta Ayatul kursiyyu, Suratul Ikhlas, Suratul Falaqi da kuma Suratul Naasi kullum da safe da yamma da kuma bayan ko wacce sallar farilla.

Mu yawaita sauraro da karatun Alqur’ani musamman ma Suratul Baqara a ko da yaushe, Addu’ar sanyawa da cire tufafi, Addu’ar shiga banɗaki “toilet”, Addu’ar cin abinci, Addu’ar shiga da fita gida da sauransu.

Kuma murika boye sirrukanmu na ni’ima da jindadin zaman auren mu ko akasin haka ga mutane kuma mu daina watsawa a social media kamar yin post ko daurawa a status saboda akwai masu kambun-baka ko kambun-Ido tayadda za su yiwa rayuwar aurenku illa…DA IZININ ALLAH.

Amma duk wannan ba su da ikon aiwatar da komai na cutar da kowa duk yadda maye ko masihirci yakai inda yakai ba za su iya yin komai ba duk sai da IZININ ALLAH..

ALLAHu A’ALAM

Allah yakara tsare mu daga sharrin dukkanin halittunsa.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »