Bani Da Lafiya Kashi Na Talatin (30)

0 538

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ummu Arqam jikinta yayi sanyi sai cewa tayi: Hasbiyallahu wa ni’imal wakeelu ! Amma wadan nan shedanun gaskiya suna zaluntar mutane wallahi, yanzu har mahaifar mutane ma suke kamawa tab dijam ! ALLAH dai yakara tsare mu da tsarewarsa.

Ummu Labeeba: Ameen ya Rabb, ai lamarin shedanun nan kadan kika gani sai dai fatan Allah yayi mana katangar karfe da su.

Ina gaya miki Sai Abu Labeeba ya dauko min sauran magungunan duk ya nuna min yadda zanyi amfani da su kamar yadda Abu Ruwaihah ya sanar da shi, ciki har da wanda zanyi wanka a cikin wata jarka yake.

Kuma ya bani wasu sharudda matukar na rike su to Insha ALLAHu Allah zai shiga lamarina kuma YAbani kariya sannan yarabani da lalurar nan cikin hikimarSA. Sharuddan su ne kamar haka:

1- Na tabbata na daina wasa da sallah, matukar ina so na samu lafiya to narika yinta akan lokaci, domin Allah yana hukunta masu wasa da sallah ne ta yadda yaso ciki har da irin wannan lalurar.

2- Na yawaita karatun Alqur’ani da sauraron Alqur’ani da Addu’ar neman waraka da lafiya a gurin Allah.

3- Na Yawaita yin Azkaar musamman na safe da maraice da na kwanciya bacci.

4- Na rika yin sadaqa akai akai da abinda zan iya komai karancinsa.

5- Na yawaita yin Istigfaari da Salatin Annabi Sallallahu alaihi Wasallama ba qaqqautawa.

Ummu Arqam: Allah Sarki, kinga magani nan ba wata wahala ko yanke yanke balle a afka ga shirka aje a hallaka kuma ayi asarar imani.

Ummu Labeeba: Wallahi kuwa yar uwa, kuma bakiji abin mamakin ba ma ai, ingaya miki ina fara amfani da maganin musmaman ma na wankan nan, duk sai naji jiki na yadda kikasan ana sabulemin wani abu daga saman kaina zuwa kafafuwa na, ai washe gari kawai sai naji ni ina bahaya wata irin kala bahayar take fitowa abin ya bani tsoro, kuma ga amai din da nake yi baki

Ingaya miki bayan wata biyu naji al’ada ta fa shiru bata zo ba, na sanar da Abu Labeeba, sai ya sanar da Abu Ruwaihah.

ABIN LURA

Lallaikam yin wanka da ruwan da aka yimasa karatun Alqur’ani irin yadda Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar, yana da matukar tasiri wajan raunata ayyukan sihiri da na kambun-baka a jikin mutum, kawai abinda akeso shi ne kayi karatun da ikhlasi da khushu’i tare da yaqinin ALLAH zai warkar da kai saboda shi kadai ne mai bayar da waraka ga wanda yaga dama kuma yahana wanda yaga dama a lokacin da yaga dama.”

(Insha ALLAHu za muji abinda Abu Ruwaihah yace a rubutu nagaba)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »