Bani Da Lafiya Kashi Na Talatin Da Daya (31)

0 521

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ummu Arqam : Masha Allah, lallaikam al’amari ya yi kyau sosai, kinga Sarautar Allah ko !

Ummu Labeeba: Ai gsky kam alhamdulillah, domin da ya sanar da Abu Ruwaihah halin da ake ciki sai yace muje asibiti, saboda shi yanzu ba fanninsa bane na likitocin asibiti ne.

Bayan munje asibitin ne sai suka tabbatar mana da cewa ina da juna biyu, Alhamdulillah allazy bi ni’imatihi tatimmus swalihaat.

Ummu Arqam: Masha Allah, lallaikam Allah ne sarki mai ikon kowa da komai, Sarkin da yake bayarwa ga wanda yaga dama kuma ya hana wanda yaga dama. Mu ma dai muna fata da rokon Allah yakawo Mana karshen wannan jarrabawar kuma ya azurtamu da hakuri a duk halin da muka tsinci kanmu ciki.

Ummu Labeeba: Ameen ya Rabb, ai kam kema Insha ALLAHu na ki yana nan tafe kawai kiyi yaqinin ALLAH ya ji kukan ki kuma Insha ALLAHu zai biya miki bukatun ki nan kusa ko nesa, kici gaba da riko da sabubban da suka tabbata a shari’ar ALLAH, indai kina da rabon haihuwa anan to za kuma kin haihu cikin hikimar ALLAH.

Ummu Arqam: Insha ALLAHu kuwa yar uwa, ina matukar godiya da wadan nan kwarin gwiwar da kike bani, Allah yasaka da alkhairi.

Maasha Allah, lallaikam ALLAH ya yi dai Ummu Labeeba tana da rabon haihuwa, shi yasa ake son kowa ya rika kwantar da hankalinsa saboda abinda Allah ya rubuta zai faru ne kadai zai iya faruwa, amma duk abinda ALLAH bai rubuta zai faru ba to fa babu abinda zai iya sanya shi ya faru.”

Suna nan a zaune ne sai ga sallamar Salaha nan makobciyar su Ummu Labeeba ta shigo tana cewa: Ummu Labeeba bakuwa kikayi ne haka?

(Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji abinda Salaha za tace game da Ummu Arqam.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »