Bani Da Lafiya Kashi Na Talatin Da Biyu (32)

0 527

Ummu Labeeba tace : Eh wallahi itama kinga matsalar rashin haihuwa ne ke damunta wallahi tsawon shekaru amma shiru ba labari.

Salaha ta juyo ta kalli Ummu Arqam sai tace: Ikon Allah… Amma dai gaskiya ina mamakin irinku wallahi, tayaya ni zan iya zama haka ba haihuwa har tsawon wasu shekaru nan nemi mafita ba.

“Su Salaha kenan wato ita ta dauka mutum ne ke baiwa kansa haihuwa ko ya hana kansa ba Allah ba, batasan babu wani mahalukin da ya isa ya tabbatar da abinda Allah bai tabbatar da shi ba duk girmansa duk iliminsa duk sanin magungunansa kuwa.”

Ummu Labeeba ta amsawa salaha da cewa: Ai itama yanzu neman mafitar ce yasa har tazo nan gidan.

Ummu Arqam dai batace komai ba, tayi shiru tana sauraron su.

Salaha: Allah Sarki, ai ingaya miki da zarar mace ta yi shekara daya ta ji shiru ba haihuwa ai akwai inda ake zuwa kuma ingaya miki yadda kikasan yankan wuka cikin satin za kiga ta samu juna-2.

Ummu Arqam dai ta kara gyara zama, amma ta kasa cewa komai sai dai wani shakku ne da maganar Salaha ta sanya mata a zuciya yake ta kai-komo a kirjinta.

Ummu Labeeba: Ikon Allah…To Salaha wane irin wuri ne kuma haka?

Salaha: Wajan malamin nan ne dai da nace zan kai ku amma kika fasa zuwa, amma mutumin yana aiki sosai kuma aikinsa yadda kikasan yankan wuka nan da nan kuma bukata take biya kiji ingaya miki.

Ummu Labeeba dai mamaki ya lullubeta har take cewa: To fah ! Amma shi ya yanayin maganinsa ne yake ?

Salaha: Ai ingaya miki ba wai wata wahala bace, kawai mushen bakar Akuya da bakin Bunsuru/Dan Akuya za a kawo ba tare da an yanka su ba, a mushen su za a kawo su.

Ummu Arqam dai hankalinta yakasa kwanciya alamun ta fahimci inda Salaha ta sanya gaba, saboda ta ga ta fara kauce hanyar Tauhidi, sai cewa tayi: Laa ilaaha illa anta subhanaka inny kuntu minazzwalimeena..! Allah ya tsare ni, ai da ace ni Ummu Arqam nayi wannan aikin don na samu haihuwa gwara na tabbata ban haihu ba har abada.

ABIN LURA

“Duk yadda ALLAH zai jarabta ku da rashin haihuwa karku kuskura kuyi masa shirka da sunan magani duk wani abinda zai kaucewa Tauhidin ALLAH kar ku kuskura kuyi shi saboda za ku shiga cikin wani bala’in da za ku gwammace ina ma ace bakuyi ba kuma ALLAH yana nan yana jiranku a lahira domin ya hukunta ku matukar baku tuba ba har kuka koma gare SHI.”

Allah yakara tsare mana imaninmu.

(Insha ALLAHu za muji ci gaban a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »