Ummu Labeeba ta kalli Ummu Arqam sai tayi murmushi take cewa: Yar uwa kenan.
Salaha kam jikinta yayi sanyi ganin yadda Ummu Arqam ke magana a fusace, sai cewa tayi: To yar uwa wannan fa ba boka bane kamar yadda kike tsammani, wannan malami ne kuma shi ma kansa baice shi boka bane.
Ummu Aqram: Hmmm ikon Allah, yoo dole ne sai ya kira kansa boka ne zai zama boka? ai aikinsa ma ya tabbatar da shi boka ne ko da kuwa ana ce masa mallam, kuma yanzu ta hakane ake lullube kwakwalen wasu mutanen sai a rika kiran bokaye da sunan malamai saboda wata muguwar manufa. Wal iyadhi biLLAH !
Ummu Labeeba itama ba shiru tayi ba sai ta kada baki tana cewa: Wato Salaha abinda zan kara fahimtar da ke game da wannan biye biyen malaman nan da kikeyi shi ne: Wallahy ki tsaya kiyiwa kanki karatun-ta-nutsu kisan cewa wannan abin ba zai taba haifar miki d’a mai ido ba, sai dai yakara jefaki halaka Kuma yayi nesa da ke daga Rahamar ALLAH tayadda za kiyi batan-bakatantan.
Salaha ta gyara zama sai tana mai cewa: Shin kema kallon haka kikeyi min ashe Ummu Labeeba?
Ummu Arqam dai taga ya kamata ta tafiyar ta in yaso daga baya sa yi maganar da Ummu Labeeba, sai tace: To Ummu Labeeba ni dai na yi gida in yaso duk abinda ake ciki zan kira ki daga baya Insha ALLAHu.
Bayan ficewar Ummu Arqam ne sai Ummu Labeeba take kara cewa Salaha: Wato Salaha a matsayinmu na makobtan juna wajibi ne mu fadawa juna gaskiya koda kuwa rayuwar mu ba ta son gaskiyar.
Taci gaba da cewa: Ganin irin haka ne ma Abu Labeeba yace na daina yin hulda da ke, har gidan nan ma ya ce kar na sake barinki ki shigo duk saboda irin wannan dabi’ar ta ki ta hulda da kuma biyebiyen bokaye da malaman tsubbu gudun kar nima ki ja ra’ayina mu taru mu lalata masa gida.
Lallaikam duk wacce kikaga tana kokarin doraki akan hanyar zuwa wajan bokaye ko malaman tsubbu to ya zama WAJIBI kuyi hannun riga da juna, ko kuma takaiki ta baro dake da imaninki duk ku rasa gane junanku.” (Insha ALLAHu a rubutu nagaba za muji yadda ci gaban yake) Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani. Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba. (Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻) Domin karin bayani: Domin Ƙarin Bayani Game Da Darrusan Marubucin.
ABIN LURA
👇👇👇
+2348031542026
https://t.me/Rismawymedicine
rismawy86@gmail.com