Bani Da Lafiya Kashi Na Ashirin Da Tara (29)

0 443

Ummu Arqam tayi ajiyar zuciya tana cewa: Hmmm ai Ummu Labeeba naga wannan matsalar kamar ma da ni ake yinta wallahy, domin duk abinda ya lissafa babu wanda ba na jinsa.

Ummu Labeeba: ALLAH sarki, wato yana kammala lissafomin tambayoyin nan sai na amsa masa da cewa: Wato Abu Labeeba maganar gaskiya a cikin wadan nan babu wanda ba na yi.

Sai cewa yayi : To shikenan ba matsala Insha ALLAHu sai na zo kenan, sai ya katse wayar.

Bayan wasu awanni sai ga shi ya shigo gida da wasu magunguna a cikin wata leda rike a hannunsa, bayan mun zauna ne sai nake tambayarsa da cewa: Yallabai lafiya dai ko?

Abu Labeeba ya amsa min da cewa: Lafiya kalau karki damu, kawai dai ya yimin wasu bayanai ne akan abubuwan da suke iya zama silar jinkirin haihuwar.

Sai nace masa: To ai nima sai kayimin bayanin su ko Maigida.

Abu Labeeba: Ai cewa yayi irin wannan matsalolin ciwon sanyin infection ma yana haifar da haka, domin idan infection yayiwa mace yawa yana iya zama PID (Pelvic inflammatory disease ), saboda shi PID wani irin ciwon sanyi ne da yake kama mahaifar mace har yaki barin ciki shiga ko kuma ya hana shi zama sai dai ayita barinsa.

Yakara da cewa: Akwai kuma Toshewar bututun “fallopian tube” ko kuma qarin mahaifa na “Fibroids”, duk wadan nan suna haddasa haihuwa tasamu jinkiri amma duk sai da izinin ALLAH.

Ummu Arqam: Ikon ALLAH kenan.

Ummu Labeeba: Ai ingaya miki ba nan Abu Labeeba ya tsaya ba sai da yace min: Kuma malamin ya ce nima dai ya kamata nasha irin nawa maganin sai ya bani wannan garin na rika shanshi da nono ( mai kyau mara tsami) saboda ina fuskantar matsalar “Low sperm count”.

Sai ya fito min da magungunan yace: Tabbas malamin ya yimin bayanin abinda ke damunki duk ba ya cikin wadan nan da ya lissafa, ya ce kina da matsalar jinnul Aashiq ne wanda yake kama mahaifar mace tayadda zai rika hana ciki shiga ko ya hana shi zama amma duk sai da izinin ALLAH.

(Insha ALLAHu za muji karin bayani a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Domin karin bayani:
👇👇👇

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »