Aloe Vera wata shuka ce da ke ɗauke da wasu muhimman magunguna, haka kuma anyi ittifaƙi cewa ruwan Aloe Vera nada daraja sosai a kowanne yanki cikin ƙasashen duniya.
Cikin amfanin nata don haka muka nemo muku yadda za’a magance cutar olsa ta hanyar yin amfani da ruwan cikin Aloe Vera.
ABIN BUƘATA:
- Aloe Vera,
- Buttermilk.
YADDA ZA’A HADA:
Zaku samu Aloe Vera ɗinku mai kyau sai a wanke ta a tsaya cikinta, sai a ɗebi ruwan cikin ta a samu kofi mai tsafta a zuba ruwan.
Za’a ɗebi ruwan kamar cokali biyu, kuma za’a iya zuba ruwa a ciki a ɗauraye ruwan nata don ya fitar da yallon dake jikin ruwan Aloe Vera ɗin.
Saiku kawo Buttermilk ɗinkimu ku zuba a ciki a juya asha kullum sau ɗaya, kuma yana da kyau a dinga sha kafin a ci abinci.
ABIN LURA:
Wannan haɗin maganin yafi amfani a Olsa maisa zafin ciki da kuma mai saka ƙwarnafi.
Allah ya bada Sa’a yankuna bada lafiya.