Yadda Zaku Mayar da Leɓanku Zuwa Kalar Ruwan Hoda (Pink Color).

0 2,346

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Sauda dama mata da kuma wasu mazan kan so ganin leɓanku yazama ruwan hoda domin yakan ƙara fito da darajar kywunsu koda kuwa namiji ne.

Wannan dalilin yasan zakaga wasu matan/mazan suna ta faman yin amfani da wasu abubuwa da basu ma dace ba domin samarwa kansu leɓe mai ruwan Hoda (pink Lips).

Wanann dalilin yasa shafin Alummarhausa ya binciko muku hanya mafi sauƙin wajen samarwa da kanku wannan kyakkyawan leɓe ta hanyar amfani da maganin da baya cutarwa.

Hanya ta ɗaya:


Abubuwan Buƙata.

  • Zuma,
  • Alumun,
  • Mai,
  • Sukari.

Zaku haɗe su gaba ɗaya saiku dunga Sanyawa a leɓen naku, kuna ɗan murzawa kamar na mintuna goma, Kuyi kamar kwana 10 insha Allahu zaku samu kyakkyawan sakamako.

Hanya Ta Biyu:


Bayan kungama goge bakinku da brush sai ku ɗauki brush din kuna gogawa a bakinku.
Yin hakan zai sanya bushashiyar fatar da ke kan leɓan fita kuma leɓan yayi kyau.

Hanya ta Uku:


Kokumba, kusamu kokumba sai ku yankata ku ɗauki sala ɗaya saiku dinga gogawa a leɓan naku sau 3 a rana na tsawon sati ɗaya.

Hanya ta Huɗu:

Ki yanka Lemon Tsaminki Saiki samu sukari kaɗan ki barbaɗa a kai Saiki dinga kokawa kullum na tsawon sati goma. Za’a samu kyakkyawan sakamako Insha Allah.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »