Muhimmancin Sanya Tafarnuwa a Ƙasan Filo Yayin Bacci

0 2,694

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Tafarnuwa na ɗaya daga cikin abubuwan dake da matuƙar muhimmanci ga lafiyar jikin dan adam. Wajen magance cututtuka iri daban dabam.

Don haka a wannan rubutu zaku samu bayanin muhimmancin Sanya tafarnuwa a ƙasan fili yayin bacci

Tana Maganin Rashin Samun Bacci Wadatacce:

Muhimmancin tafanuwa
Don samun ingantaccen bacci

Sauda dama wasu kan wahala a lokacin da suke da buƙatar su samu suyi bacci, zasuyi ta juyi da tunane tunane haka kawai.
To Ka nemi tafarnuwa kwara daya ka daga filonka, sai ka saka ta a kasa. Zata baka damar yin bacci mai daɗi.

Tana Magance Yawan Firgita Yayin Bacci:

Wasu mutanen kan firgita lokacin da suke tsaka da bacci, wanda wani idan yayi wannan firgitar takan sanya masa tsoro ya kasa komawa bacci,

Tana Ƙarawa Gangar Jiki Lafiyar:


Jiki ba dutse bane samun isasshen bacci kan bawa gangar jiki kuzari,

Ka shafe tafarnuwa da man habba sai ka karanta ayatul kursiyu kafa uku ka tofa sai ka sakata a ƙarƙashin filo ka konta. Maganin shaidanun aljannu na dannau da zasu zo a cikin baccinka su tausheka kana ji ka na ta faman ihu a baccinka amma ka gagara motsa jikinka ko magana.

Tana Magance Wasu Ciwon Jiki:

Kasamu tafarnuwa ƙwaya daya kaci kafin ka kwanta a sanda kake fama da ciwo a jiki ka, sai kuma ka saka ƙwara daya a karkasahin filon ka kwanta akai to zaka wayi gari da karfin jiki ba kasala ba ciwon jiki, amma kada a ci abinci sosai a yayin da za’a kwanta bacci. Hakan na haifarda kumburin ciki dama lalacewar ciki.

Jiƙa Tafarnuwa

Ka jika tafarnuwa kwara daya da ruwan zamzam ka ajiye sai in zaka kwanta bacci sai ka sha zatayi maka maganin cututtuka da dama a jikin ka, sannan kumaZaka rinƙa jin lafiya da karfi a jikinka insha Allah.

Yawan Tasowar Farfaɗiya ya:


Idan farfadiya na yawan taso maka da dare ka nemi tafarnuwa busasshiya ka karanta suratul jinn kafa uku sai ka tirare jikinka da ita.

wannan kaɗan kenan daga cikin muhimmancin tafarnuwa

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »