Yadda Zaa Magance Ciwon Hanta.

0 3,349

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ciwon hanta (Hepatities B) rashin lafiya ce da kaco kan dinta hanta ne take illatarwa, ta kan lalata hantar dan adam, ta haifarda cutuka da dama da za su ci zarafin hantar har ya kai a lokacin da bata iya aiwatarda aikin nata waton (liver failure)

Wasu Daga Dalilan Dake Jawo ciwon Hanta:

  • Hanyar jima’i da mai ciwon.

Anan idan lafiyarka lau sai ka sadu da mace mai ciwon hanta to lallai cutar zata same ka domin akwi wasu vaginal secretion da za su iya kutsawa zuwa a cikin jijiyoyin zakarinka daga nan ciwon ya samu hanya kenan.


Haka ita ma maccen da take lafiya lau idan ta sadu da namiji mai ciwon hanta to zata iya daukar ciwon ta maniyinsa.

  • Ruwan Gyambo


Idan ruwan gyambon mai ciwon hanta suka kutsa zuwa a cikin jikin wanda baya daukeda ciwon to zai iya kamuwa da ciwon hanta.

  • Yawun Baki


Haka kuma ana daukar ciwon hanta ta yawun mai ciwon kamar ta sumbata ko wata hanya ta daban.

  • Jini Ko Ruwan Mai Cutar

Idan ruwan jikin mai ciwon hanta ko jininsa ya kai ga kutsawa ko suka gauraya da ruwa ko jinin jikin mutumen da baya daukeda ciwon to shi ma zai iya kamu da ciwon hanta.

Albasa
Albasa

Yadda Za’a Maganin Ciwon Hanta Da Kuma Dakatar Dashi Daga Yaɗuwa.

Abubuwan da Zaka Tanada:
Albasa,
Zuma,
Ruwa Gallon Daya (litre),
Sai ƙaramin kofi.

Mataki Na Daya Kan maganin Ciwon Hanta:
Za’a samu Albasa guda shida (6) manya sannan ka yayyanka su kamar zaka yi miya.

Mataki Na Biyu:
Sai ka samu ruwa galan guda (5litre) sai ka raba shi biyu…..

Sai ka dauki rabin ruwan wato (2.5litre) sai ka dafa albasar ka da rabin ruwan…

Mataki Na Uku:
Bayan ka gama dafa albasar ka sai ka tace albarsar sai kazubar da albarsar sannan sai ka dakko rabin ruwan da ka ware sai ka hada shi da rabin da kadafa albarsa kaga ya tashi galan guda kenan (5litre)….

Mataki Na Hudu:
Sai kasamu zuma mai kyau sai ka samu ƙaramin kofi irin na silver din nan sai kariƙa cika ƙaramin kofin kana dibar Zuma din cokali 3 kana zubawa cikin ƙaramin kofin kana sha sau uku a rana har sai ruwan ya ƙare da zumar….

Mataki Na Biyar:
Bayan ka gama kaje gurin likita ya gwada ka….

Kuma ina roƙon yan uwa musulmi a yada wannan abin, Allah yabada lafiya mai ɗorewa Amin.

Daga: Maganin Gargajiya

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »