Amfanin Sabara Wajen Kara Lafiyar Jikin Dan Adam.

1 3,666

Sabara da Turanci ana kiranta ‘Guiera senegalensis’ amma an fi saninta da ‘Moshi medicine’.

Sabara tana fitowa da kanta, ba tare da an shukata ba a guraren yashi da cikin sahara. Tana da koren ganye da ‘ya’ya masu kalar yalo da gashi mai laushi ajikinsu.

Ana iya mafani da Saiwar Sabara da ganyenta da kuma yayanta.

Ga Wasu Daga Cikin Ayyukan Sabara Wajen Kara Lafiya

Idan aka samu Sabara, aka cirota, wato da saiwarta da ganyen da yayan da itacenta gaba daya, to tana maganin

Don Magance Cutar Kansa (Cancer).


Ana iya daka sabara, a dinga zuba garinta rabin cokali acikin nono, a sha kullum sau daya, tsawon kwana goma zuwa sati biyu don magance cutar kansa.

Don Kashe Guba:


Wanda ya sha magani ba bisa ka’ida ba, ‘wato overdose’, in yana gudun maganin ya cutar da shi, ko wanda ya sha guba ko kayan maye, to zai iya jika sabara a ruwa ya sha, domin tana hana gubar da ke cikin magani ta cutar da mutum.

Tana Magance Gumin Dare:

Wanda yake da matsalar gumin dare, idan yana jika garin Sabara yana sha zai samu waraka, insha Allahu.

Tana Magance Cutar Gudawa:


Saiwar Sabara da kuma ganyen Sabara, suna taimakawa sosai wajen magance matsalar gudawa ga yara da manya.

Tana Maganin Basir:


Ana tafasa Saiwar Sabara, idan ta dan huce sai a sha, don magance matsalar basir.

Tana Magance Tsargiya:


Mai matsalar fitsari da jini, idan yana shan saiwar Sabara itama tana warkarwa.

Tana Maganin Kuraje:
Sabara na maganin cututtukan da ke kama fata, kamar kuraje da dai sauransu.

Tana Taimakawa Mata Wajen Ni’ima:
Sabara na taimakawa wajen saukarwa da mata ni’ima.

An san Sabara kuma an jinjina mata wajen magance matsalolin Aljanu da na sihiri.

Ana iya shan garin Sabara daga cokali daya zuwa kasa a wuni guda, ba tare da ya cutar da mutum ba.

Daga cibiyar Sunnah Medicine,

  1. […] post Amfanin Sabara Wajen Kara Lafiyar Jikin Dan Adam. appeared first on Alummar […]

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »