Halima Yusuf Atete wacce akafi sani da Halima Atete shaharariyar yar wasan Hausa ce kuma mai tsara finafinan, wanda mafiya yawan fina finanta takan fito ne a fim na Annamimanci ko Kishi.
An haifi Halima Atate a ranar 26 ga watan Nuwanbar shekarar alib 1988, a garin Maiduguri dake Jihar Barno a Najeriya.
Halima Atete tayi makarantar Firamari ta, Maigari Primary School, sanan tatafi makarantar gwabnati ta Yerawa Government Secondary School. Jarumar bata tsaya a iya nan ba ta wace makarantar gaba da Secondary inda ta samo kwalin National Diploma a Shari’a and Civil Low.

Tauraruwar ta shiga Kamfanin shirya Finafinan Hausa dake Kano a Shekarar 2012, yayin da ta fara Fim dinta na farako mai suna Asalina.
jarumar ta fito a Finafinai sama da guda Dari da Sittin (160).
Atete tasamu girmamawa da dama a masana’atar inda mafiya yawancin girmamawar tana zuwa ne daga City People Entertainment, sai daya daga African Voice.