An haifi Isma’il Isah Funtua a ranar 17 ga watan Janairun alib 1942, a garin Funtuwa, dake Jihar Katsina.
Yana daya daga cikin daliban da suka fara shiga makarantar Federal Training Center Kaduna. Ya samu horon zama Jami’in Gudanarwa a Tsangayar Nazarin Ayyukan Gudanarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya da kuma karatun ayyuka na gudanarwa a Jami’ar Manchester dake kasar Ingila.
Daga baya kuma ya yi aiki a ma’aikatu da dama a tsohuwar Gwamnatin Jihar Arewa. Da ga bisani kuma sai ya koma Masakar UNTL da ke Kaduna, inda yake kula da ma’aikatan kamfanin masu yawa
Ya taba rike Ministan Albarkatun Ruwa a karkashin Gwamnatin marigayi Shehu Shagari, haka kuma shine mamalaki kuma darakta a kamfanin yin tufafi na Masakar Funtuwa.
Haka kuma shi ya kafa kamfanin New Africa Holdings Limited, wanda suke wallafa jaridar nan mai suna The Democrat Newspaper.
Marigayi Isma’ila Isa Funtua yana daga cikin iyayen Makarantar Koyon Aikin Jarida ta Kasa-da-Kasa Wato (International Press Institute) da Kungiyar Editoci ta Qasa-da-qasa wato (Global Network of Editors and Media Excutives).
Marigayi Isma’ila Isa jajircaccen dan siyasa ne na jamaa kuma ba mai surutuba domin kuwa bashi da wani buri sai ganin kan yan Najeriya ya hadu guri guda tare da samun aiyuka na more rayuwa.
Isma’il Isah ya rasu yana da shekara 78 a duniya,