Yadda Mata Zasu Gyara Nonuwan Su Da Suka Kwanta

0 5,481

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Nono yakan kwanta ne ta hanyoyi iri daban daban wasu nonuwansu kan kwanta sakamakon shayarwa da suke ga yaran su, wasu kuma kan kwanta ne saboda wani yanayi musanman yan matan dabasuyi aure ba.

wannan rubutu zai miki bayanin yadda kwantaccen Nonanki zai dawo kamar na budurwa.

ABUBUWAN DA ZAKI NEMA.

  • Farar Shinkafa.
  • Jar Masara.
  • Alkam.
  • Gero.
  • Nono ko
  • Yogot.

YADDA ZAKI HADA WADANNAN MAGUNGUNA.

Kisamu farar Shinkafa, Jar Masara, Alkam, Gero. sai ki wanke su ki shanyasu su bushe saiki soyasu sama-sama sai a nika miki su, amma kuma zaki iya dakawa idan kina da karfin haka.

Sai ki tankaɗe bayan an nikasu kenan ko an daka, bayan kin tankade din saiki samu Nono mai kyau ko kuma Yogot mai kyau sai ki ɗebi wannan garin naki da kika tankaɗe kamar cokali ɗaya da rabi ko biyu sai ki dinga zubawa a wannan Nono naki ko yogot saiki juya sosai ki shanye.

Wannan haɗi insha Allahu indai matsalar kwanciyar Nono ce ta kawo karshe, Nonuwanki zasu dawo kamar na sabuwar budurwa, kuma zasuyi laushi da yaddar Allah .

Allah ya bada ikon yi kuma a Turawa yan Uwa Mata don Suma su amfana.

ABIN LURA:

Idan kinsan zakiyi yaye Kada kiyi, ki bari sai kinyi yayen kin gama war kewa daga cutar da ake fama da ita ta yayen yara , sai kiyi.

Wannan shine bidiyon zaku iya kalla kai tsaye

A TURAWA YAN UWA SUMA SU AMFANA

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »