Ana so ko da yaushe idan mijinki zai kusance ki yaji ki a matse kike, ba”a son lokacin da miji zai kusanci matarsa ya wuce siririf.
Don haka ya ke da kyau mace ta rika kula da gabanta kar ya bude
Abubuwan da ke matse mace suna da yawa misali
- Bagaruwa.
Ana dafa ta da ganyen magarya ko ita kadai a rika wanke gaba dashi ko ki zuba a baho ki zauna a ciki da dumin kaman 30mins a kalla sau biyu a sati.
- Kanunfari
Ana dafa shi a sha da zuma da zafi zafi ko ki jika ya kwana da safe ki tace kisha da madara da zuma.
Ana kuma dafa ta a zauna a ciki da dumin ta ko a rika tsarki da ruwan ko kuma a zuba kanun farin garwashi a tsugunna shi ma sau 2 a sati.
Kina iya samun kanumfari koda kwaya daya ne saiki sanya a bakinki kina taunawa a hankula har ta kare, Shi kima wannan zai sanya bakinki kamshi na kanumfari kuma koda kina da matsalar warin baki zai dena kinga kenan zaki iya kissing dinsa yadda kike so.
- Kwallon mangwaro
Idan kika fasa zaki ga dan ciki fari haka, ana busar dashi a daka a kwaba da zuma arika matsi da shi bayan isha’I idan zaki kwanta bacci ki wanke ko kuma ki dafa dan cikin da bagaruwa ki wuni tsarki dashi ko ki zauna a cikin shima a kalla 3x a sati.
Almiski fari ko ja ki daka kanunfari ki tankade yai laushi sai ki kwaba da miskin da man zaitun yawaita amfani dashi na matse mace sosai kuma kullum cikin kamshi….
Yana gyara macen da ta haihu sosai musamman da jinin haihuwa ya dauke ki fara amfani dashi har ki ar’bain…
Inda wannan ta faru dake Zaki iya tsarki da
- Ruwan dumi
- Bagaruwa
Na tsawon Wata guda sai kuma matsi shi kuma zakiyishi saura sati biyu aurenki kuma wannan mun dade dayin bayaninsa
Muna godiya