FARKON KAFUWAR MASARAUTUN KASAR HAUSA 2

0 765

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

A wanCen Darasin mungama da na 1 don haka yanzu Zamu dora zuwa na 2

A farko-farkon shekaru na 1900’s, a sa’adda kabilar Hausa ke yinkurin kawar da mulkin angizo na fulani,sai turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka mamaye arewancin Nijeriya, da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida,a bisa karkashen mulkin birtaniya,’yan mulkin mallaka sai suka marawa fulani baya na cigaba da manufofin angizon siyasarsu, har yanzu dai mulkin kamin gambiza tsakanin Hausawa da Fulani shi ne yayi kane-kane a arewacin Nijeriya.

Wannan hadakar gamin kambiza, an farota ne tun asali a matsayin fulani su dare madafun ikon a tsararren tsarin siyasar arewa.Akasarin masu mulki na fulani sun kasance yanzu, a al’adance hausawa gwamitse. Amman duk da haka akwai wata masarauta daya tak a arewacin Nideria, wadda itace masarauta daya tilo da babu birbishin milkin Fulani a cikin ta. Wannan masarauta itace masarautar Daura dake jihar Katsina.

Babban abin lura anan shine; tarihi ya tabbatar da cewar kasar Hausa ta fara mulki sama da shekaru dubu biyu kafin haifuwar Annabi Isa (A. S); haka ma ta kafu shekaru dubu kafin zuwa ko bayyanar Bayajidda a Daura. A wancan lokacin babu wani abu wai shi mulki ko shugabanci, wanda sai daga baya ne aka fara gudanar da karbabben mulki irinsa na farko.

Ko tababa babu, a duk lokacin da za a bayyana tarihin asalin mulki a kasar Hausa, to sunan kasar Daura ne zai bayyana a sahun farko, domin masana tarihi da masu biye da tarihi sun yi ittafaki tare da tabbatar da cewar Daura ce tubali kuma ginshikin mulkin al’ummar Hausawa tun da can da a dubun-dubatar daruruwan shekaru da dama da suka gabata.

A wancan zamanin bakidaya al’ummar kasar Hausa kowa zaman kansa yake yi, ma’ana babu shugaba ballantana shugabanci. A haka wani bawan Allah wanda ake kira Abduldar ya zo ainihin tsohon garin Daura (Kilomita 7 daga Arewacin Daura ta yanzu) Ya kuma zo ne daga kasar Libya, yayin da aka so a dauki ransa. ( A wancan lokacin Libya tana karkashin Masar) Abduldar da ne ga Najib, mahaifinsa ne ke sarauta a Masar, Najib kuwa, Lamarud ne mahaifinsa, wanda shine Sarki a Kan’an, Kan’an kuwa ai Annabi Nuhu A.S ne mahaifinshi.

Abduldar kuwa Sarki na biyar daga Annabi Nuhu, ya kuma bar inda yake mulki ne ya zo kasar Libya. Bayan zuwansa Daura, jama’ar yankin sun rika mutuntawa tare da girmamashi, musamman bisa ga ganin launin jikansa ba irin nasu ba ne.
Al’ummar Daura, sun ci gaba da yi wa Abduldar, biyayyar yi-nayi bari-na- bari har ya zama shugaban al’ummar yankin bakidaya. Hasalima shine asalin shugabanci a kasar Hausa. Sarkin na farko yayi shugabanci ne har zuwa rasuwarsa.

A kan wannan ‘yarsa ta gaje shi a matsayin Magajiya ta farko; ta yi nata mulkin ne har zuwa rasuwarta. Daga nan ne jama’a suka yanke shawarar cewar tun da sun ga mulkin namiji da na mace, sun kuma fi jin dadin mulkin mace, don haka suka aminta da matsayar mata ne za su rika mulkinsu. A kan wannan ne mata suka zama Sarakuna Daura na farko. Ga bakidaya mata 17 ne suka mulki al’ummar Daura, mulki na tsayin sama da shekaru 900.

Marigayi Wakilin Tarihin Masarautar Daura, Muhammad Siya Abubakar, tsohon Malamin Makaranta, kuma tsohon kantoman mulkin karamar hukumar Daura, bugu da kari, san nan shugaban kungiyar masu karbar fansho, ta jihar Katsina, ya zayyanasu kamar haka;
Mata daya bayan daya da suka yi mulki a kasar Daura, sune;

  • Kufuru
  • Ginu
  • Yakumo
  • Yakunya
  • Wanzamu
  • ’Yanbamu
  • Gizir-gizir
  • Inna-Gari
  • Daurama
  • Ga-Wata
  • Shata
  • Fatatuma
  • Sai-Da- Mata
  • Ja-Mata
  • Ha-Mata
  • Zama
  • Sha-wata

Daga cikinsu idan wannan ta kaura wata ce za a nada a matsayin Sarauniya, duka daga cikin zuri’arsu. Daurama ta farko, ita ce ta 9 a cikin jerin Sarakuna Mata. Daurama ta karshe kuwa ( Daurama Sha-Wata) a lokacin mulkinta ne Bayajidda ya zo kasar Daura. Bayan rasuwar Daurama, an aminta da cewar duk Sarauniyar da za a nada, za a fara kiranta da sunan Daurama, daga nan sai ainihin sunanta na yanka ya biyo baya.

Domin a can da Magajiya ke sarauta, daga baya kuwa ai Daurama ce. Wakilin tarihi ya bayyana cewar “A lura masana tarihi kan bayyana cewar Bayajidda ya tarar da Daurama tana mulki. Sai dai abin lura tare da gyara a kundin tarihi shine ba ainihin Daurama ta asali ce ya tarar ba, a’a, Daurama Sha-Wata ce ya tarar, wato ta 17. Mata Sarakuna guda takwas ne suka yi mulki, bayan Daurama ta farko.”
Bawo dan Sarauniya, jikan Bayajidda, wanda shi kansa yayi sarauta a Daura, ‘ya’yanshi ne suka yi sarauta a kasashen Hausa Bakwai, wato Daura da Katsina da Kano da Zariya da Rano da Garun-Gabas da kuma Gobir. Sarki Gazaure shine ya gaji Bawo a Daura.

Shi kuwa dan baiwa, jikan Bayajidda ‘ya’yansa ne suka yi mulkin garuruwan da a can da ake kira Banza Bakwai, a yanzu kuwa ‘yan uwa Bakwai.

Kasashen ’Yan uwa Bakwai dai su ne, Kabi da Yawuri da Zamfara da Ilorin da Nupe da Gwari da kuma Kwararrafa. Tun dai daga ranar 31 ga Oktoba, 2011, Mai Martaba Sarkin Daura na yanzu, ya shelantawa duniya haramcin amfani da kalmar Hausa Bakwai da Banza Bakwai, sai dai Hausa Bakwai, da ‘Yan Uwa Bakwai. Illa iyaka!
A cikin fadar mulki ta farko aka nada Baghauda dan Bawo aka kuma turashi a matsayin Sarkin Kano na farko. Kuma a cikinta ne aka nada dan Bawo, jikan Bayajidda a matsayin Sarkin Katsina. Haka kuma a cikinta ne aka nada ‘ya’yan Bawo jikokin Bayajidda, wato Gunguma, da Duna, a matsayin Sarakunan Zariya da kuma Gobir.

Shi kuwa Zanna-Kogi dan Bawo, yayansa Baghauda ne ya rike shi, daga baya kuma ya nada shi Sarkin Rano na farko. A nan mai karatu zai tuna da wakar Mamman Shata inda yake cewa

“Mai Rano Garba Autan Bawo.”

MARUBUCI;:

IDRIS MUHAMMAD AHMAD, AL-AZHAR UNIVERSITY CAIRO EGYPT

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »