TARIHIN KOFOFIN ZAZZAU (ZARIA) KASHI NA BIYU

0 4,260

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

TARIHIN KOFOFIN ZAZZAU (ZARIA) KASHI NA BIYU

 Idan kuna biye damu a rubutun baya wato Kashi na daya muntsaya a kofa ta BIYAR don haka yanzu zamu kawo muku ragowar. 

KOFAR KONA:
An ce ana kiranta da suna Kofar kona saboda ta cikinta Malaman Kona suka shigo Zariya. Shi kona wani kauye ne da akace wasu malamai suka kafa.

Asalin sunasa An ce ya samu ne lokacin da malaman suka zo shigewa suna neman wurin zama, sai shugabansu ya lura da kyawun wurin, don haka yake tambayar sauran malaman cewa ‘ko nan zamu zauna?’ Sai suka amsa masa da gamsuwar zama a wurin.

Daga baya da akazo ginin ganuwa sai shashin garin ya shigo cikin birni, don haka suka yanke shawarar barin kauyen nasu na Kona tare da komawa cikin Zazzau da zama.

Wadannan sune tsoffin kofofin da akace sun jima a Zazzau, amma daga bisani an samu fasa wasu kofofin kamar su Kofar Jatau, Kofar Galadima da kofar Matar-kwasa wadda akafi kira da Sabuwar kofa. 

KOFAR JATAU:
Masana tarihi sun ce an rada wa wannan kofa sunan wani Sarki ne a mulkin Habe mai suna Isiyaku Jatau, wanda ya ja silin mulkin Zazzau daga shekara ta 1782 zuwa shekara ta 1802. Wasu bayanai kuma sun ce sunan wani mayaki ne mai gadin kofar Jatau da aka sa kuma hakan ya faru ne a zamanin Sarkin Zazzau Jatau.

KOFAR GALADIMA:
Wannan kofa, masana tarihi sun ce an sa mata sunan Galadiman Zazzau Daudu ne. Shi Galadima marokan fadar Sarkin Zazzau na yi ma sa kirari da “Galadima, Daudu rana da hazo kofar birni”, wato abin nufi shi ne shi mutum ne da ako wane lokaci hannunsa a budde ya ke ga marokan fadar. 

Wasu masana tarihi kuma sun bayyana cewar, an sa wa wannan kofa sunan Galadima Dokaje ne. A duk zantukan nan biyu waDanda suka yi karo da juna, an dai yanke hukuncin sunan wannan kofa dai Kofar Galadima. A cewar masana tarihin, an sa wa kofar sunan Galadima ne kasancewar gidansa na kusa da inda kofar ta ke.

KOFAR FADA:
wannan kofa da ake kira da sunan kofar fada ita ce fadan-fada, wadda ke kofar gidan sarkin zazzau na yanzu, wato inda ake kira da Fada.
wannan kofa tun zamanin sarakunan Habe aka gina ta, duk kokarin samun tubalin wannan kofa ya gagara, sai dai masana tarihi sunce,  wannan kofar ita ce dai kofar da ake bi wajen shiga gida sarki wadda ke a Fada ta 

KOFAR HAURE:
Kofar haure na nan tsakanin kofar jatau da kofar kuyanbana, a yau zamu iya cewa, kofar haure na nan a bayan unguwar da ake kira rimin danza. sarki makau shine sarkin zazzau na karshe a jerin sarakunan habe guda sittin (60) da suka mulki masarautar zazzau.

Dalilin bude wannan kofa shine, lokacin da ayarin rundunar mujadadin addinin islam na shehu bn fodio karkashin jagorancin malam musa bamalle suka iso zariya, sarki makau ya fahimci cewar, shi da rundunar mayakansa bazasu iya yakar wannan runduna ta tawagar musulmi ba, sai ya yanke shawarar gudu, shine yazo yasa aka sare masa badalar (ganuwa) inda ake kira daga baya da hauren majema, yasa aka sare masa badalar don ya fita ta nan, gudun kada a fahimci ta inda ya fita. 

kamar yadda aka sani, wannan fita da sarki makau yayi, shine musabbabin kafa garin zuba da kuma Abuja wanda ke masarautar zazzau na suleja a yanzu haka.

ALHAMDULILLAH KUYI KOKARIN TURA AIYUKANMU TA HANAYR AMFANI DA SOCIAOL MEDIA DAKE KASA

Kofofin zazzau kashin na 1

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »