KAZAURE
sun kasance farkon mazaunan ƙasar da ake kira Kano. Labarin tarihin Kazaure ya nuna labarin yadda Kutumbi a daya daga cikin farautar nemansa ya sami kwari kewaye da babban fili da wadata tare da kõguna da ƙoramu. Ya zauna a yankin don yankin yakasance shuru babu hayaniya ya zauna a wurin zuwa wani lokaci har sai da iyalinsa suka damu da dadewar rashin sa sakamakon bai saba fita farauta yayi irin wannan dadewar ba.
Don haka sai suka yanke shawarar bin hanyar da yabi don tafiya wannan farauta kasancewar rashin dawowarsa sun bi hanyansa har tsawon kwanaki. Bayan dogon lokaci suna tafiya, sun sami Kutumbi a kwari mai kyau.
Kutumbi da danginsa sun kasance a yankin suna rayuwar su daruruwan shekaru, sun bar dubin kayan tarihin kayansu na farauta da kuma kayan da suke amfani dashi tun na wancen lokacin na Harkokin al’adu. Sun kuma aikata kananan aikin noma.
Wanda ya kikireta sahine Dan Tunku ne, Jarumi a kabilar Fulani wanda yake daya daga cikin masu dauke da tutar 14 Jahadi na Fulani shugabanta Usman Dan Fodio.
Ya karbi tutar daga Shehu. Bayan haka ya taimaka kafa Fulani a Daura, amma daga bisani ya sami ba ta taka muhimmiyar rawa a jihadi ba ya ba da gudunmawa ga nasarar masu gyarawa Kano. Da ƙarshen yaki ya kasance a arewacin Kano.
KU KASANCE DAMU A KASHI NA BIYU (2)