KASAR HAUSA
Kasar Hausa kamar yadda tarihinta ya zo a litattafai da dama,suna alakantata da mazaunin Hausawa na farko kafin su watsu zuwa sassa daban-daban na duniya.
Mu’azu (1993:1) ya bayyana ainihin kasar Hausa ta asali da” tana Afirka ta yamma ne, a farfajiyar da ke tsakanin hamadar sahara da kuma dazuzzukan da suka doshi gawar tekun atlantika, watau daga kudu.Kuma ana kiran kasar da sunan Sudan ta yamma,watau tafkin Chadi da kuma gwiwar kogin Kwara a can yamma.”
A wani kaulin kuwa Dokaji (1978) ya bayyana kasar Hausa da kasa ce da ta dade da wanzuwa a yammacin afirka wadda kuma ba a iya hakikance lokacin fara wanzuwarta.
Related Posts
A cewar wasu masana, kasar Hausa ita ce yankin nan na kasar Sudan wanda ke wajen tsakiya-tsakiya.
Daga gabas da ita akwai kasar Borno, daga yamma kasar Dahomey (wacce yanzu ake kira jamhuriyar Benin), daga arewa hamadar sahara, daga kudu kuma kasashen da ake kira “Middle belt”
Alhasan (1982) Ya ce asalin kasar Hausa ya faro ne daga kauyukan Lalle da Asodu da ke arewa maso gabas da Agadas can cikin kasar Nijar.
Daga can Gobirawa suka taso kadan kadan suka taru a muhallinsu na yanzu da ke cikin arewacin Nijeriya.
DAGA LITTAFIN:- TASIRIN MAWAKAN BAKA WAJEN HABAKA AL-ADUN HAUSA
IBRAHIM MUHAMMAD (DAN MADAMIN BIRNIN – MAGAJI)
Wannan tarihi ya fa’idantar sosai. Allah ya kara habaka Hausa, ya kuma kare Hausawa.