KASHI NA HUDU
A shekarar 1948 Sa’adu zungur ya tafi Lagos don fafutikar kafa Jam’iyyar Al’ummar Nigeria ta Arewa JANA (JANA), anan ne kuma ya zamo akawun jamiyyar NCNC tasu Dr Azikwe.
A likacin kuma sai waɗancan kungiyoyi na arewa suka sake kiran zaman tattaunawa na biyu a Jos, wanda anan aka haɗu akan ya kamata a kafa kungiyar cigaban yankin Arewa mai suna ‘Northern Progressive Congress’ (NPC).
Wani Likita mai suna Dr R.B Dikko ne ya zamo shugaba, sai su Yusuf Maitama Sule, Abubakar Imam, Sa’adu Zungur, Aminu Kano, Yahaya Gusau, Dr. Rafi da sauransu suka zamo a kunshin jadawalin shugabannin kungiya.
A shekarar 1949 aka kama Habibu Abdullahi Raji da wasu mabiya kungiyarsa ta NEPA aka garkame a kurkuku bisa zargin su da sukar mulkin turawa ta hannun sarakuna, aka kuma cigaba da muzgunawa duk wani da yake aibanta Turawa ko sarakunan gsrgajiya.
Sai dai duk da haka, ‘yan boko basu karaya ba tunda a shekarar 1950 kungiyar NPC ta shirya zaɓe a kano, anan ne kuma manyan mutane suka shigo ciki waɗanda ake ganin sarakuna ne suka ingizo su domin karɓe ikon kuɓgiyar tare da dakushe haskenta, anan aka shiga zaɓe kuma aka kawar da matasa irin su Yusuf Maitama Sule waɗanda aka kafa kungiyar dasu daga kunshin shugabanci.
Ana haka sai NPC ta soma rabuwa gida biyu, ya zamo ana samun saɓanin ra’ayoyi, da rashin fahimta musamman sa’ar da Mai-Martaba marigayi Sarkin Kano na Lokacin Abdullahi Bayero ya bayar da lasisin kafa Sinima a kano, sai wasu sukace hakan daidai ne, wasu kuwa suka ce ba dai-dai bane, wannan abu tozarci ne ga addini, suka shiga rubuce-rubuce suna sukar abin.
Ana cikin haka Sai a shekarar 1950 wani mai suna Bello Ijemu ya bada shawarar kamata yayi akafa jamiyyar siyasa, ya kira masu ra’ayi irin nasa mabiya kungiyar NPC irinsu Abba Mai kwaru, Yusuf Maitama sule, Magaji Dan Baffa, Baballiya Manajan Banki da wasunsu suka kafa jamiyyar NEPU ranar takwas ga watan takwas da mutum takwas.
Wannan jam’iyya ta NEPU, ana iya xewa manufofinta kachokan adawa yake da sarakunan, tunda kullum cakakinsu don me shugabancin jama’a zai zama gadon-gadon maimakon a bajeshi mai bukata ya tsaya zaɓe kamar yadda kasashen da sukaci gaba sukeyi a duniya.
Daga nan kuwa sai adawa ta soma shiga tsakanin kungiyar NPC da jamiyyar NEPU. ‘Yan NPC sukace sun haramtawa duk wanda yake Kungiyar NPC yin NEPU, suka kuma samu goyon bayan sarakuna sannan suka rikiɗe izuwa jamiyyar siyasa.
A lokacin, Maitama sule da Aminu kano da wasu suka bar NPC zuwa NEPU, shikuma Sa’adu zungur ya bar NPC ya cigaba da zamansa a NCNC. Sai fa adawa da sukar juna ta shiga tsakani, mabiya na zagi da cin mutunci.
Haka siyasa taci gaba da tsamari a Arewa, kowanne ɗan siyasa na ganin yafi ɗanuwansa kishin Arewa da kokarin samar da cigaba a yankin. Haka kuma a lokacin da Sa’adu Zungur ya kai shawarar cewa ya kamata jam’iyyar sa ta NCNC tazo ta haɓaka ilimi da rayuwar matasan arewa, sai yaga shugabanninta sunyi fatali da abin. Wannan yasanya shi dogon nazari tare da barin jam’iyyar, ya gane ashe ra’ayin ‘yan kudanci kurum yake karewa, gashi kuma jahilci yayi katutu a Arewa,mutane da yawa sunfi gane suje duyi karta su likawa masu molo kuɗaɗensu, basu cika maida kai ga abinda ya shafi cigaban yanki ba.
Bayan dogon nazarin abinda ya kamata yayi, sai kurum ya rera shahararriyar wakar nan mai suna ‘Arewa Jamhuriya Ko Mulukiyya’ domin farkar da mutan Arewa kada su bari ‘yan kudanci su hau kansu su danne..
👇🏿👇🏿👇🏿👇🏿👇🏿👇🏿👇🏿
- KARANTA TARIHIN SIYASAR NIGERIA 🇳🇬 KASHI NA DAYA
- KARANTA TARIHIN SIYASAR NIGERIA 🇳🇬 KASHI NA BIYU 2
- KARANTA TARIHIN SIYASAR NIGERIA 🇳🇬 KASHI NA UKU 3
Bashir Tukur G