TARIHIN GARIN MALUMFASHI TA JIHAR KATSINA

2 1,430

Get real time updates directly on you device, subscribe now.


Kirarin Garin Gangara Ta Naturɓe, idan ka ji ina kwana bako ne.. Sai dai Nyalli Jam.
Wannan gari tsoho ne, jimawarsa kuma har ta kai wasu na ganin ya girmewa tsoffin birane misalin Malumfashi, Getso, Batsari da Birnin Kano.
Fulani kabilar Natirawa ne a ka ce su ka kafa garin lokaci mai tsawo da ya shude, sannan labari na gaskiya ya dusashe dangane da tsohon birnin, ko kuma lokacin kafuwarsa, wanda a yanzu ya zama kufai, amma dai zuwa yanzu an iya gane sashen ganuwar tsohon birnin. Haka kuma marinar garin da tsoffin kukoki na nan a inda tsohuwar rayuwar Natirawan ta afku shekaru daruruwa da su ka gabata.
Babban limamin garin mai suna Malam Adamu, ya bayyana ma na cewar an samo sunan garin ‘Gangara’ ne daga kalmar ‘Gagara’, ko kuma a ce garin da ya gagara a lokacin yaki, domin tunda wannan birni ya ke babu wani sarki da ya taba cin sa da yaki.
An samu cewa garin Gangara na usuli shahararre ne, mai zagaye da ganuwa, mai dauke da tarin mutane kuma. Mutane na zuwa fatauci daga sassa daban-daban na kasar Hausa. Har ma an ce akwai zamanin da sai da gidaje su ka cika birnin, har ma wasu su ka rika yin gidaje a bayan ganuwa.
Sannan kasancewar garin na Fulani ne, akwai tsohuwar al’adar nan ta sharo da kuma wankan amarya da a ka ruwaito ta na wakana tsakankanin mazauna birnin, amma dai an ce Musulunci ya samu karbuwa tun kafin zuwan Mujaddadi Usmanu Danfodiyo, don haka abubuwa irin na maguzanci ba su yawaita ba.
A batun yake-yake, garin Gangara ya yi zarra, tunda an ce akwai wani katon kada mai suna ‘Nabogaji’ wanda ya ke cikin wani tafki dake kusa da garin, wanda kuma ya ke rura kuka yayin da wani bala’i ya tunkaro garin domin sanar da mazauna birnin su yi shiri.
Dukkan maruwaitan tarihin garin Gangara sun hadu a kan cewa babu wanda ya taba cinye garin da yaki. Wasu sun ce da zarar Nabogaji yayi ruri, sai idanuwan mahara ya rufe, ya zamo ba sa iya ganin birnin da abinda ke cikinsa, yayin da wasu ke ganin tsabar jarumtar sadaukan birnin ke ba su ikon mayar da keyar mahara baya.
An ce Gangara ta taba kaiwa garin Getso hari, ta ci nasara a kan garin, har sai da ta kori maza da mata da ke garin. Haka kuma Gangara ta yi yaki da garuruwan Matazu, Kurkujan na Musawa da Malumfashi a baya-bayan nan, kuma duk ta samu nasara.
Liman Mallam Adamu ya fada mana cewar asalin garin Malumfashi Gangara ne. Domin kuwa zamani mai tsawo daya wuce, an taɓa yin wata annoba ta ciwon ciki wadda mutanen birnin Gangara su ka rinka mutuwa. Don haka sai mutanen suka tashi izuwa gefensa su ka kafa sabon gari, yayin da wadansu suka fantsama sassan duniya.
To an ce daga irin wadannan mutanen ne wani Banatire mai suna Dano (ko Dunu ) ya riski garin Malumfashi a lokacin ya na jeji. Sai ya sauka sannan ya sari gona domin ya dan taba noma. Da amfanin gona yazo, sai ya zamana ya samu alheri, don haka ya shiga godiya ga mai sama ya na fadin “Yanzu Na- numfasa”.
Daga nan kuma sai labari ya iso garinsu Gangara, inda mutane su ka rika tafiya inda ya ke da zummar su je su yi noma su samu riba da kubuta daga waccan annoba. Don haka sai suma suka rinka cewa “zamu tafi inda Dano yake Munumfasa” watau mu huta daga wannan annobar. 
Daga baya aka maida sunan garin ya koma ‘mulumfashi’ ko ‘Malumfashi’. A cewar Liman, babbar hujja akan haka shine unguwar Gangarawa dake garin malumfashi. Wadda babu wata
tsohuwar unguwa data girme mata.
Sunan sarautar garin Gangara shune ‘dan-saka’, ance ta samu ne daga wani sarkinta mai sakawa duk waɓda aka yiwa zalunci daga talakawansa. Hak kuma kasancewar sunayen tsoffin sarakunanta sun ɓata, amma dai an samu cewar a  baya bayan nan sarakuna irinsu:-
Dan saka Atiku, Dan saka Babba, Dan saka Nani, Dan saka Isiye, Dan saka Bello zarɓe magajin tunkuda, dan saka sarki ya-musa, dan saka yuguda, da dan saka muhammadu magajin dadi duk sun mulketa, sai kuma dagacin dake mulkinta ayau mai suna Magaji Alh Bala Dan Muhammadi Majidadi.
Koda yake, ance yanzu sarautar dansaka ta koma garin Gora bisa tashin tsohom dan saka Muhammadu majidadi daga Gangara zuwa garin na Gora saboda tsangwamar natirawa, don haka da aka turo dansa sai ake masa lakabi da Magaji. Saboda hak yanzu sunan sarautar garin ‘Magaji’.
Sannan kuma har gobe mutanen garin Gangara suna fahari da cewar Mujaddadi Shehu Usmanu ya sauka a garin akan hanyarsa ta zuwa kano daga sokoto, harma ya sahale aka soma sallar juma’a a garin, a lokacin da duk yamma da kano daga Rimin Gado, sai malumfashi ake zuwa yin sallar jumu’a…
Zuwa yanzu dai, garin ya na nan a kusa da garin Dayi, kuma ya na karkashin karamar hukumar Malumfashi ne ta jihar Katsinan Nijeriya.

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

  1. Abdul says

    Tnx

  2. Hausa People says

    Yayi

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »