Amfani Da Zogale Wajan Ajiyar Wake Domin Gujewa Kwari.

0 96

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Wannan rubutun zai matukar taimakawa iyaye mata a cikin gida ko ma wasu yan kasuwar maza da mata in sha ALLAH._

Da yawan mutane ba sa son siyan wake da yawa sbd tsoron ajiye shi na wani lokaci, sbd kwari za su iya lalata shi, wasu kuma dole sai sun sanya masa maganin kwari ko dai wani chemical din dabam matukar suna son su ajiye shi zuwa wani lokaci gudun kar kwari su lalata shi.

To yanzu ga wata mafita nan da aka samo ta hanyar gargjiya ba tare da anyi amfani da Chemical ko wani maganin kwari wajan ajiyar wake ba.

GANYEN ZOGALE kawai za ku samu da dama sai a zuge/zare shi daga iccensa sai a zuba shi ( ba tare da an hada shi da komai ba) a cikin waken a barshi haka a cikin waken IN SHAA ALLAHu wannan tsarin zai yi sanadin da babu kwarin da zasu iya zuwa wajan wakenka balle su lalata shi, har lokacin da za ku kara amfani da shi.

Ku gwada haka wannan hanya ce mai sauki kuma wacce ta fi wannan Chemical din da ake sanyawa.

Allah yasa mudace

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »