Bani Da Lafiya Kashi Na Arbain Da Daya (41)

0 441

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

ABIN LURA

“Idan ma’aurata na fuskantar matsalar haihuwa kuma aka fahimci mijin ne ke da lalurar, to abinda ya kamata matar tayi shi ne: Ta sanyawa rayuwarta cewa wannan jarabawa ce daga ALLAH kuma tayi ta Addu’a musamman ma ta Istikhaara, Insha ALLAHu da sannu ALLAH zai bata mafita wacce ta dace da ita. Amma ba wai ta hakikaice akan lallai ilalla ita dole sai an sake ta taje ta auri wanda yake haihuwa ba, da yawa-yawan masu yanke irin wannan hukuncin kai tsaye sai dai kaga sun kare a jiya iyau ko kuma gwara jiya da yau saboda abinda ake nema ya ki samuwa.”

Abu Arqam: Allah Sarki. Lallaikam kowa da irin tasa matsalar. Alhamdulillah alaa kulli haalin.

Abu Ruwaihah: Wallahy kuwa Dan uwa, amma sunyi maganin fa har sun gaji, har sai da tattalin arzikin su ya girgiza saboda neman magani kuma har yanzu dai jiya iyau ba wani sauyi.

Ummu Arqam: Kai jama’a ! Ni kuwa wane irin yanayi ne matar nan za ta kasance a ciki ?

Abu Ruwaihah: Ai kam rikicewa tayi a gidan tana cewa: Itafa haihuwa take bukata, ba za ta iya zama a haka ba, gsky ya sauwake mata taje ta samu haihuwa a wajan wani, saboda duk ga sa’anninta nan kowa da yaransa amma su ga su nan sunfi shekaru 10 amma har yanzu shiru ba wani labari.

Abu Arqam: Allah Sarki, gaskiya na tausayawa mijin saboda bansan wane irin hali take son ta jefa shi ba?

Abu Ruwaihah: Ai wallahy ni kaina na yi kokarin fahimtar da ita akan ta nemi zabin ALLAH amaimakon neman sakin nan da take yi kai tsaye.

Ummu Arqam: Ai mallam abinne wallahi ba dadi, ku maza za ku iya jurewa amma mu mata ba kowacce ce za ta iya jurewa ba, saboda a cikin kawaye ma wallahy wasu da gangan za suyi ta jefa maka maganganu idan har ba ka kai zuciya nesa sai mutum ya afka cikin wani yanayi ta yadda zai salwantar da Imaninsa gaba daya wajan nemo haihuwa ta ko wane irin hali. Kaico…

(Insha ALLAHu za muji ci gaban tattauanawar a rubutu nagaba)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »