Bani Da Lafiya Kashi Na Arbain Da Biyu (42)

0 27

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Abu Arqam: Eh lallaikam don wannan akwai wannan, amma sau da dama ku mata kuna manta cewa ita fa haihuwa ta ALLAH ce mutum bai isa ya baiwa kansa ko ya baiwa waninsa haihuwa ba, dole sai ALLAH ya so.

Ummu Arqam tayi murmushi sai cewa tayi: Ai Abu Arqam ba fahimta ta za kuyi bane yanzu, saboda ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne.

Abu Ruwaihah : ALLAH Sarki, ALLAH yakara tsare mana imaninmu.. In karkare muku batun su dai mutanen nan a haka suka rabu a ƙarshe ya sahale mata auren nasu ya rabu har taje tayi wani auren, duk da kuwa a baya ya yi kokari iya kokarinsa amma abin ya ci tura.

Abu Arqam: Ka ga gajen hakuri ko..

Ummu Arqam: Wane irin gajen hakuri kuma anan, tayaya ba ta jin dadin zaman kuma an gano shi ne ke da matsala sai tayi ta zama tana cutar da kanta kenan ?, Ai a irin haka ma sai kaga shedan ya sa ta jefa kanta cikin wani mummunan hali na biye biyen maza.

ABIN LURA

“A irin haka idan lamari yafaru ya kamata mahukuntan bangaren miji da na matar su baiwa kowanne hakkinsa, ita matar idan har tana son rabuwa da mijin ne domin ta je ta samu haihuwa a wani wuri to sai su rabu irin rabuwar da Addini yayi tanadi, amma barinta anan kamar tauye mata hakki ne ake yi, idan kuma taga za ta iya zama shikenan fani’imah wannan kuma ra’ayinta ne hakan, amma kar a kuskura a ketare Shingen Allah.”

Abu Ruwaihah: Kwarai kuwa, domin irin hakan ya taba faruwa ne da wasu ma’auratan makobtansu shi yasa itama take jin tsoron kar shedan ya yaudareta ta afka cikin halaka…

Wato lamarin makobtansu ne wallahy abin ba dadin ji, domin a karshe sai da ita matar makobcinsu din ta kawo masa cikin-shege kuma aka haife shi a gidansa shikuma yana daukarsa a matsayin Dan cikinsa akan rashin sani. Kaico

Abu Arqam: HaashaliLLAH ! To ita kuma a garin yaya har ta bari hakan ta faru da ita tana musulma?

Abu Ruwaihah: To mutumin Attajiri ne babba yana da dukiya da kuma manyan kadarori, amma sai Allah ya jarabce shi da wata cuta har takai bazai iya samun haihuwa ba, shi ne ita da iyayenta suke son haihuwa tare da shi saboda su gaji dukiyarsa.

(Insha ALLAHu za muji ci gaban bayanin a rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »