Bani Da Lafiya Kashi Na Arba’in (40)

0 29

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Ummu Arqam : Kwarai kuwa mallam, ai ko kafin ma mu yarda muzo wurinka sai da muka tabbatar da yadda kake bayar da maganinka muka ga babu shirka ko wani surkulle a cikinsa shi yasa ma muka amince.

Abu Arqam shi ma yakara da cewa: Ai Mallam, ni farko ma ban yarda azo ba saboda ni dai na fawwalawa Allah lamarinSA, wata kila ba mu da rabon haihuwar ne anan Duniya.

Abu Ruwaihah yayi murnushi sai yake cewa: Allah Sarki, ai Qaddarar kowa tana a hannun Allah samu ko rashi, karka fitar da rai, kai dai ka dau duk wani sababin da ya kamata a dauka wanda yayi daidai da shari’ar Muslunci wanda yake ba shirka ko ketare iyakar Sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, idan kana da rabo na tabbata za ka samu lokaci ne kawai za a jira, idan kuwa ba ka da rabon to fa dole sai dai a dau dangana.

Abu Arqam: Kwarai kuwa, wannan haka yake shi dama mummuni kullum cikin kyautatawa ALLAH zato akasanshi, kuma har kwanan gobe muna kan wannan turba kuma muna kara rokon ALLAH yatabbatar da mu akanta har bayan rayuwarmu.

Abu Ruwaihah: Ameen ya Rabb. Wato dan uwa, ku ai ma ku godewa Allah tunda har binciken likitoci ya tabbatar muku kowannenku kalau kuke ba bu mai matsala, domin wasu da suka taba zuwa nan wurin wallahy idan kukaji sai lamarin ya baku tausayi da takaici.

Ummu Arqam: Subhanalllah ! Me ya faru da su ne kuma haka Mallam ?

Abu Ruwaihah: Ai su da suka je Asibitin sai aka nuna cewar Mijin ne ba shi da lafiya saboda haka ba lallai ne ya iya haihuwa ba a hakan dole ne sai ya magance matsalar tukunna.

(Insha ALLAHu za muji ci gaban bayanin q rubutu nagaba.)

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »