Shin Ko Kunsan Tauna Ganyen Zogale Da Kabeji Na Maganin Olsa

0 669

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Idan mutum ya samo ganyen zogale ya zuge shi kuma ya yayyanka cabbage (kabeji ), sai ya wanke su ya tsaftace su da kyau, sai ya rika taunawa yana hadiye ruwan safe kafin yaci abinci sai kuma da dare kafin kwanciya bacci.

Duk mai fama da ciwon Ulcer yarika yin haka ko da yaushe har na tsawon watanni uku in Sha ALLAH zai rabu da cutar kwata kwata daga jikinsa.

Ammafa ganyen danye ne za ayi amfani da su ba sai an dafa su ba kuma ba a sanya musu komai su kadai kawai za arika taunawa, kawai wankewa za ayi.

Allah yasa mudace Kuma yakara mana lafiya mai amfani.

Har kullum mu rika tabbatarwa da zuciyar mu cewar: Magani sila ne na waraka amma ba shi da ikon warkarwa, Allah ne kadai mai iya warkar da wanda yaga dama a duk lokacin da yaga dama, shi kadai ne abin dogara ba maganin ba.

(Ayi mana Addu’ar ALLAH ya yarda da mu da ayyukanmu kuma ya lullube mu da RahamarSA.🤲🏻)

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »