Sanadin So ( Kashi na 3 Hausa Novel )

0 106

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

SANADIN SO KASHI NA UKU

Daga wayar nayi tare da yin sallama, aka amsa daga daya bangaren. Samari kai ne saurayin Fateema ko? Aka tambayeni. Kafin amsa maka tambayarka, zan so sanin matsayinka ga Fateema. Mahaifinta ne ni. Aka bani amsa sai bayan ya bani amsa, nayi nadamar yi masa tambayar, kayi Hakuri Abba ban san kai ne ba shi yasa, Ni ne masoyinta na bashi hakuri tare da amsa masa tambayarsa.

Munyi magana da ita akan ta fitar da wanda zata aura tace kai ne zabinta shine na karbi lambarka a wajenta. Haka ne, na amsa masa ina so ne in ganka muyi magana saboda haka ka sameni gida gobe da sassafe.

To! Abba sai dai ban san gidan ba. Ok bari zan turoma da adireshin gidan yanzu. Cike da farin ciki muka yi sallama da shi. Na dade ina jinjina al’amarin a cikin raina bayan na gama karanta adireshin gidan, wai dama ashe da diyar kwamandan soja nake soyayya ban sani ba.

An ya ban kira ruwa ba kuwa? Na dade ina shawara da zuciyata, daya sashen zuciyata na cewa kar ka je Hussain daya kuma na cewa kaje me zai faru idan kaje, don mahaifinta na soja ai ba zai dakeka baka yi masa laifin komai ba, daga karshe dai na yanke shawarar zanje komai ta fanjama fanjam. Wannan shi ne ganganci mafi girma da na taba aikatawa a rayuwata. Uhm
waiyo rashin sani
Tun a lokacin nayi ta kokarin kiran layin fateema amma yaki shiga, ina son fada mata wannan albishir ne duk da na san ta rigani sani, a WhatsApp ma sako uku ina tura mata ba reply. Daga karshe dai nace a raina wata kila caji ne babu a wayarta. WASHE GARI DA SAFE Gabana na faduwa na cusa kan babur dina cikin Barikin soja wannan shine karo na farko da na taba shiga barikin Sojoji.

Bayan tulin tambayoyin da na sha daga sojoji barkatai, aka sadani da gidan Kwamandan. Bayan na samawar wa babur dina matsugunni a kofar gidan, sai naje ga kofar na kwankwansa, wani mataccen Soja ya leko, ke ce bakon oga? Ya tambayeni da gurbatattar Hausarsa. Eh ni ne, na bashi amsa. Kai tsaye ya budemin kofa na shigo ya nunamin wata kujerar roba ya ce in zauna, zamana ke da wuya sai ga wasu samudawan sojoji guda biyu wadanda tunda nake a duniya ban taba gani sojoji kakkarfa kamar su ba, sai ji nayi sun rufeni da duka da wasu kulake, suka yi ta dukana har sai da suka sumar dani..

Sanyin ruwan da aka zubamin shine yayi sanadiyar farfadowata daga suman da nayi.wanda ba zan iya tantance iya adadin lokacin da na dauka a some ba, har yanzu dai. Samudawan nan ne tsaye bisa kaina.

Shegiya kwarton oga yau zaki ci ubanki, tashi.kiyi sallen kwado suka umarceni da
gurbatattar Hausarsu..

Naga ta kaina ba irin nau’in azabar da basu ganamin ba a ranar, har sai da nayi dana sanin zuwana duniya, basu kyaleni ba sai da suka tabbatar bani da sauran mamora a tare dani sannan suka kwasheni kamar kayan wanki suka zube a wani matsakaicin daki wanda nake zaton na maigadi ne.

Sai a lokacin nadama ta fara zomin, na tuna yanda mukayi da abokina LOCY, ba yanda bai yi dani akan in kyale yarinyar nan ba, amma naki daga karshe ma da naga ya takuramin sai cewa nayi dashi yana bakin ciki ne dani don yaga na tsinci dami a kala.

ko jiya sai da muka sha fama dashi yana
kokarin hanani zuwa ni kuma nace sai na je sai yanzu na gano illar rashin bin shawara a lokacin fa ruwa ya kare wa dan kada bai gama wanka ba.

Ina cikin wannan sake-saken najk an bude gambun dakin, kallo daya nayi masa na fahimci ko shi waye dogo ne mai faffadan kirji yana sanye da suit baka akwai sanko a kansa yana da tsawon fuska, shekarunsa zasu doshi sittin.Kwamanda ne. Kayi kuskure dan samari neman matar soja, kuma a sojojin ma matar kwamanda. Duk da yanayin da nake ciki na azaba hakan bai hanani dago fuska na kalleshi cikin kaduwa ba ina mai jaddada girman maganar da ya fada a raina.


WATA SABUWA… WAI DA MATAR AURE NAKE SOYAYYA ASHE.

ZANCI GABA DA PART 4 GOBE INSHA ALLAH.

Ab Kudancy

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »