Sanadin So ( Kashi na 2 Hausa Novel )

0 188

SANADIN SO KASHI NA BIYU

DA YAMMACI.. Yau ma kamar kullum bayan mun gama gaisawa da fateema a WhatsApp sai take cewa dani. In tambayeka mana. Ina jinki. kana da aure?.

Na shafe kusan minti uku ina nazarin tambayar tata, ko zan gano dalilinta nayi min wannan tambayar amma ban gano ba, daga karshe dai na bata amsa tare da jefa mata tawa tambayar No i’m single, but why asking? ( A’a bani da aure, amma kuma me yasa kika tambayeni?) shiru ne ya ratsa tambayar tawa, har na tsawon minti goma, da dai naga shirun yayi yawa sai na sake tura mata wani sakon Hello! Fateema kina kusa kuwa? Eh! Ta amsa. min, Na rasa yanda zan baka amsar tambayarka ne. Saboda me? Na sake tambayarta.Ina jin nauyin fitar maganar ne daga bakina, saboda ban san yanda zaka dauketa ba Tace dani.

Feel free fateema Just express your mind (kar ki ji komai kawai ki fadi abinda ke ranki).

Ba zan boye maka komai ba… wutar soyayyarka ta dade tana ruruwa a zuciyata, har ta kai ga yi wa zuciyata mummunar illah, irin illar da in har baka bani daukin gaggawa ba, ko shakka babu tarwatsewa zata yi. Jin maganar tata nayi a wani bambarakwai, na jini duk wani wani iri, saboda wannan shi ne karo na farko a rayuwata da wata ‘ya mace ta taba furta min kalmar SO, hasalima ni ko soyayya bana yi.

Bakina da ‘yan mata gaisawar mutumci. Shiru taga yayi yawa, ta kauda shirun da Hello! Ko maganata ta bata maka rai ne? In na bata maka rai kayi hakuri, nayi ta kokarin danne damuwata a zuciyata, na kasa ne shi yasa na fito fili na fada maka……

Ko daya fateema baki batamin rai ba, hasalima farantamin rai kika yi, ai ko da wasa mutum yace yana sonka ya gama maka komai, ballanta kyakkyawa kamarki, kuma Babbar yarinya In takaice muku zance.

A ranar muka kulla yarjejeniyar Soyayya, muka aminta da zukatan Juna.


Tun daga ranar da muka kulla soyayya da fateema, abin ya sauya salo, saboda a koda yaushe muna makale da juna, idan bama Chatting to waya muke. RASHIN SANI YAFI DARE DUHU… WATA SAFIYA….. Kamar kullum yau ma Chatting muke da Masoyiyar tawa sai musayar kalaman soyayya muke a tsakaninmu ta WhatsApp, sai nake cewa da ita.


My dear kin san wani abu kuwa? No! my one sai ka fada. Idanuwa na sun kagauta suyi tozali da kyakkyawar surar nan taki, kunnuwana cike suke da daukin jin sautin muryarki kai tsaye ba wani shamaki a tsakaninmu, hancina ya kagauta da ya shanshani kamshim turaren jikin abar kaunata, yaushe ne mafarkin nan nawa zai zama gaskiya? Ka yi hakuri my one!, idan baka manta ba a ranar da muka fara haduwa na fada maka ina da wata damuwa har ka bukaci in fada maka damuwar nace ka bari in lokaci yayi zaka sani, yanzu lokacin da ya kamata in sanar da kai wannan damuwar.

Hakika iyayena sun zabamin miji wanda ni kuma ba abinda na tsana a duniya kamarsa, shi yasa a duk lokacin da na tunashi sai inji gaba daya duniyar tayimin kunci, ba mai yayemin wannan kunci sai kai da labaranka, fahimtar da suka cewa na tsaneshi shi yasa suka sakamin tsatstsauran mataki na hani hulda da kowane irin namiji, ka kuwa ga yanzu haduwarmu da kai akwai matsala, amma na fara shawo kan iyayen nawa sun fara gano illar da ke tattare da auren dolen da suke so su yimin, sun fara yin sanyi, saboda haka ka kara hakuri da na ida shawo kansu, suka janye waccan maganar, to a lokacin sai ka gaji da ganina.


My dear kenan, dama masoyi yana gajiya da ganin masoyiyarsa ne? Ina rokon Allah Ya nuna mana lokacin da matsalarmu zata yaye.


Ameen cewarta.
Na gama sakankancewa a zuciyata cewa nayi gamo da katar, kuma hakana yana gab da cimma ruwa, wai ashe da sauran rina a kaba.


Kwana biyu da yin wannan maganar, ina shago bisa kekena ina dinki, wayata ta fara kururuwar neman agajina, ina dauko wayar kiran wata bakuwar lamba na gani. Nayi dana sanin daga kiran nan, Wallahi da na san za’a yimin wannan kiran da banyi fatan mallakar waya a rayuwata ba. WANNAN SHI NE BABBAN KUSKUREN DA NA TABA TAFKAWA A RAYUWATA.

Kubiyo mu a part 3 gobe idan Allah yakaimu.

Ab Kudancy

Leave A Reply

Your email address will not be published.

Translate »